Connect with us

MANYAN LABARAI

June 12: Shin Sabuwar Ranar Dimukradiyya Za Ta Amfani Najeriya?

Published

on

A ranar Laraba 6 ga Yuni, 2018 ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayar da sanarwar cewa, daga yanzu Najeriya za ta rika  yin bikin Ranar Dimukradiyya ta kasar da a ke yi shekara-shekara ne a ranar 12 ga Yuni, wacce ta zo daidai da ranar da a gudanar da zaben da a ka yi amannar cewa, Marigayi Cif MKO Abiola ne ya lashe shi a 1993. Tabbas wannan sanarwa ta yi matukar faranta rayukan ’yan Najeriya na asalin yankin Kudu maso Yamma, wato yankin Yarbawa kenan, inda Abiola ya fito. To, amma abin tambaya a nan shi ne, shin wannan sanarwa da me za ta amfani ’yan kasar bakidaya kuma mene ne rashin alfanunta? Kowane abu dai ya na iya zamowa mai amfani a wata fuska, yayin da a wata fuskar kuma ya ke iya zama maras amfani. Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya duba bangarorin biyu.

 

Amfanin June 12 A Matsayin Ranar Dimukradiyya:

  1. Wanzar Da Tarihi

Tarihi wani ginshiki ne na kowacce irin al’umma, domin ya na taimakawa wajen gina makomar jama’a bisa la’akari da abinda ya faru a baya. Batun ‘June 12’ wani abu ne wanda ya ginu kuma ya kafu ya samu guri a tarihin Najeriya da siyasarta. Wanzar da wannan tarihi tare da hana shi shudewa ta hanyar tsayar da ranakun 12 ga Yuni na kowacce shekara a matsayin Ranar Dimukradiyya ta Najeriya, abu ne wanda zai dada assasa tarihi a kasa kuma zai sake fito da abubuwa fili ta yadda jikoki da tattaba-kunnen rayayyun ’yan Najeriya na yanzu za su samu abin dafawa wajen dora makomar kasar a kan ginshikin da ya kamata da kuma ciyar da ita gaba, sannan hakan zai zame mu su sandar kiwo wajen la’akari da inda a ka fito da kuma inda ya kamata a dosa. Kowacce al’umma wanzuwar tarihinta ya na matukar muhimmanci wajen dora cigabanta.

 

  1. Karfafa Dimukradiyya

Yadda a ka yi imanin cewa mafi yawan ’yan Najeriya ne su ka fito su ka zabi Cif MKO Abiola shekara ta 1993 a matsayin shugaban kasa daga kowanne yanki na kasar, amma a ka soke zaben, tabbas hakan ya kashe jikin talakawan kasar kan aminci da dimukradiyya da ’yancin da ta ba su na zabar abinda su ke so a kansu, don kashin kansu. Karrama waccan rana wacce wasu ke ganin cewa a ranar ne a ka yi sahihin zaben da ba a taba yin kamarsa ba, wani abu ne wanda zai karfafa dimukradiyya a Najeriya.

 

  1. Bai Wa ’Yan Gwagwarmaya Kwarin Gwiwa

Ganin yadda ’yan gwagwarmaya su ka kwashe shekaru su na nunin yatsa kan wannan batu na soke zaben 12 ga Yunin 1993, girmama wannan rana a matsayin ranar dimukradiyya a Najeriya zai bai wa ’yan gwagwarmayar neman ’yanci karfin gwiwar cewa ko-ba-dade ko-ba-jima a na iya yin nasara, idan a ka jajirce a ka cigaba da yin ta. Don haka karrama wannan rana da gwamnatin Buhari ta yi zai karfafi gwiwar ba su kansu ’yan gwagwarmayar June 12 kadai ba, a’a, hatta ’yan gwagwarmayar da su ka biyo baya za su samu irin wannan karfin gwiwar cewa koami daren-dadewa nasara na nan tafe.

 

  1. Kashe Gwiwar Azzalumai

Daya daga cikin alfanun da a ke ganin wannan sabuwar Ranar Dimukradiyya a Najeriya za ta kawo shi ne kashe gwiwar azzaluman shugabannin da ke aikata murdiyar zabe da sauran ayyuka na zalunci, saboda ganin yadda bayan kimanin shekara 25 da murde zaben da a ke yi am sa kallon a matsayin halastacce, amma yanzu an tuna da ranar a matsayin ranar dimukradiyya, wanda hakan ke nuni da cewa, ba a aminta da matakin da su ka dauka na zalunci ko soke zaben ba. Don haka nan gaba irin makamancin zaluncin ba wanda zai sake samun karfin gwiwar aikata shi.

 

Illar June 12 A Matsayin Ranar Dimukradiyya:

  1. Karin Kashe Kudi

Sanya sabuwar Ranar Dimukradiyya a Najeriya ya haifar da bukukuwa guda biyu a kusa da juna duk shekara, domin ranar 29 ga Mayu ce ranar da a ke rantsar da shugabanni a Najerita, wanda hakan ke nufin cewa, shugabannin za su cigaba da gudanar da bukukuwa a wannan rana, don bayyana irin ayyukan cigaba da kokarin da su ka yi a kowacce shekarar da ta shude. Bugu da kari, masu adawa da shugabannin su kuma za su yi nasu nazarin na nuna cewa ba su gamsu da yadda su ka gudanar da mulkinsu a shekarar da ta gabata ba. Hakan ya na nufin kuma cewa, bayan ’yan kwanaki kalilan kuma za a sake gudanar da wani bikin a kasar na Ranar Dimukradiyya, wacce ta yiwu 29 ga Mayu zai fi zame wa shugabannin abu mai dadi, domin kai tsaye su abin ya shafa. Wadannan bukukuwa guda biyu tabbas za su janyo karin kashe kudin a hukumance, wanda hakan ya fi kusa da barnar dukiyar kasa.

 

  1. Kawo Rudani

Sauya ranar 12 ga Yuni zuwa Ranar Dimukradiyya a Najeriya tare da bai wa Marigayi MKO babbar lambar karramawa ta kasa, wato GCFR, waccan wadanda su ka shugabance kasar a ke bai wa yawanci, da kuma bai wa wanda ya tsaya wa Abiolan takarar mataimakin shugaban kasa, Babagana Kingibe, lamba ta biyu mafi daraja a kasar, wato GCON, na nuni da cewa tamkar sun taba mulkar kasar ne (duk da cewa tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ya taba bai wa Obafemi Awolowo). Don haka me ya sa a za a ba su fanshon da tsofaffin shugabannin ke amsa ba? Shin meye matsayin sakamakon zaben na June 12? Idan har gwamnatin Buhari ta na nufin ta halasta shi ne, to me ya sa ba za a damka wa Kingibe mulki ya idda aniyarsu shi da Marigayi Abiola ba? Idan kuma ba a nufin Abiola da Kingibe sun mulki kasar, to meye matsayin Bashir Tofa, wanda ya kara takarar shugabancin kasar da Abiolan a 1993 din? Tunda dai ba a sanar da wanda ya lashe zaben ba har zuwa yau din nan, domin soke shi a ka yi, me ya sa ba za a karrama Bashir Tofa kamar yadda a ka karrama Abiola ba, domin a idon dokar kasa gabadayansu ’yan takara ne har sai an sanar da cewa wane ne ya lashe zaben a hukumance? Bugu da kari, anya waiwayen abinda ya riga ya wuce da nisa, ba zai rika dawi da hannun agogo baya a Najeriya ba? Shin irin su Kingibe ba za su iya yin amfani da wannan dama su garzaya kotuna, don halasta wancan zabe tare da neman a rantsar da su ba? Irin wadannan rudanin na iya tasowa a dalilin wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka na saka June 12 a matsayin Ranar Dimukradiyya a Najeriya.

 

Bayyanar Fifikon Bangaranci

Wasu sassa na Najeriya na iya ji a ransu cewa an fifita bangaren yankin Kudu maso Yamma, wadanda a ke kallo a matsayin ’yan-baka a siyasar kasar, domin yawancin sassan kasar su na irin tasu damuwar, amma ba a waiwaye ta an biya mu su ba, sai yankin Yarabawa. Misali a nan shi ne, kowa ya san yadda yankin Kudu maso Gabas, wato kasar Ibo (Inyamurai) ke fafutukar ganin an mika ma sa mulkin kasar, an kuma yafe tare da mance yakin basasa da ya haifar shekaru aru-aru da wuce, amma babu wata alama da ta nuna cewa za a cika mu su wannan buri, domin hatta kujerar mataimakin shugaban kasa ba su taba samu ba tun da a ka fara wannan Jamhuriya ta Hudu. Ba Ibo ne kadai ke da irin wannan damuwar ba, amma muhimmin abu a nan shi ne, irin wannan biyan bukata da wasu ke kallo a matsayin ta yanki na iya zama silar da wani yankin zai iya yin bore.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: