Connect with us

WASANNI

Juventus Ce Za Ta Lashe Kofin Zakarun Turai, In Ji Ronaldo

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Juventus ce za ta lashe kofin zakarun turai na wannan shekarar duba da yadda kungiyar take da manyan ‘yan wasa.

Ronaldo ya bayyana hakane a jiya a shirye shiryen da kungiyarsa ta Juventus din ta keyi na buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Balencia dake kasar Sipaniya a wasan farko na rukuni rukuni na gasar ta wannan shekarar.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce dai ta lashe kofin na kakar wasan data gabata lokacin da Ronaldo yana buga wasa a kungiyar sai dai bayan komawarsa Juventus, Ronaldo ya bayyana cewa yana da yakinin cewa Juventus ce za ta zama zakara.

“Bayan na dauki lokaci ban zura kwallo a raga ba a sabuwar kungiyata na damu matuka sosai saboda yadda mutane suke surutun cewa nabar Real Madrid kuma na daina cin kwallo na fara damuwa sosai amma yanzu kuma komai ya wuce” in ji Ronaldo

Ya ci gaba da cewa “Ina godiya ga ‘yan uwana ‘yan wasan Juventus wadanda suka taimaka min na fara gogewa a sabuwar kungiyata da kuma sabuwar gasa kuma ina fatan nan gaba kadan zanci gaba da samun nasarar cin kwallaye”

Juventus dai ta samu nasarar lashe wasanninta guda hudu data buga a gasar Siriya A kuma tuni ta zama ta daya akan teburin gasar ta siriya A.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: