Connect with us

WASANNI

Juventus Ta Amince Za Ta Ba Manchester United Dybala

Published

on

Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta amince zata bawa Manchester United dan wasanta Paulo Dybala domin ta karbi dan wasa Paul Pogba kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An bayyana cewa dai Pogba bayajin dadin zama a Manchester United bayan da suka samu rashin jituwa tsakaninsa da mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Manchester United Jose Mourinho inda har takai ya ajiyeshi a wasu daga cikin wasannin kungiyar na kakar wasan data gabata.

Tuni dai Jubentus ta ware kudi kusan fam miliyan 150 domin siyan dan wasan wanda yabar kungiyar Shekaru uku da suka gabata kuma tuni Jubentus din ta amince zata bawa Manchester United Dybala domin samun saukin cinikin.

Dybala dai bayajin dadin zaman Jubentus tun bayan da dan wasa Cristiano Ronaldo yakoma kungiyar hakan yasa kawo yanzu wasa daya aka fara dashi a a kungiyar kuma dan wasan yafara tunanin barin kungiyar.

Dybala dai yafara tunanin  barin Jubentus a watan Janairun shekara mai zuwa idan har aka samu kungiyar da zata siyeshi sai dai Jubentus batason barin dan wasan yatafi sai an kammala kakar wasa.

Kungiyoyin Barcelona da Real Madrid da Manchester City ma suna zawarcin dan wasa Dybala wanda hakan yasa Manchester United sai ta sake dagewa sosai idan har tanason ganin ta siyi dan wasan mai shekara 24 a duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: