Juventus Ta Sake Samun Koma Baya A Siriya A  

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sake samun koma baya bayan da tayi rashin nasara a gidan kungiyar kwallon kafa ta Atalanta a wasan mako na 31 a gasar Serie A da suka kece raini ranar Lahadi.

Juventus ta buga wasan ba kyaftin din tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo wanda ke yin jinya wanda wasu suna ganin yana daya daga cikin dalilan da suka sanya kungiyar tayi rashin nasarar.

Juventus ta kasa ratsa bayan Atalanta wadda ta dage sai ta hada maki uku a kan mai rike da kofin na Serie A amma rashin dan wasa Cristiano Ronaldo ya bawa kungiyar gagarumar matsala sosai a fafatawar.

Daga baya Juventus ta koma tsare gida, ko ta tashi da maki daya, idan ba a yi nasara a kanta ba, sai dai saura minti uku a tashi daga fafatawar dan wasa Ruslan Malinobskyi ya zura kwallo a ragar ta Juventus wadda tsohon dan wasanta, Andrie Pirlo yake koyarwa.

Da wannan sakamakon kungiyar Atalanta ta koma ta uku a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Juventus ta hudu mai maki 62, bayan buga wasanni 31 a kakar wasa ta bana da ake kokarin kammalawa.

Wannan kuma shi ne karon farko da kungiyar ta Atalanta ta yi nasara a kan Juventus, bayan sama da shekara 20 wanda hakan ba karamin koma baya ya bawa kungiyar ta Juventus ba wadda aka fitar daga gasar cin kofin zakarun turai na bana.

A wannan matakin Juventus wadda ta yi harin lashe Serie A na bana na 10 a jere ta kwan da sanin hakan da wuya, bayan da Inter Milan ta daya ta ba ta tazarar maki 13 bayan itama Inter Milan ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Napoli a karawar mako na 31 ranar Lahadin inda suka tashi 1-1 .

Kungiyar kwallon kafa ta Lazio wadda take ta shida a teburin gasar bana tana da kwantan wasa daya da tazarar maki hudu tsakaninta da Juventus kuma hakan yana nufin idan Juventus tayi wasa zata iya rasa matakin da take kai a yanzu.

Ranar Lahadi, Lazio ta doke Benebento da ci 5-3 kuma wasa na biyar da ta yi nasara a jere a gasar Serie A kenan, ita kuwa Bologna nasara ta yi a kan Spezia da ci 4-1 ya yinda AC Milan ta doke Genoa da ci 2-1.

Exit mobile version