Daga Rabiu Ali Indabawa
Kungiyar dake fafutukar kare hakkin Bil’Adama SERAP ta roki Shugaba Buhari da ya gudanar da binciki kan yadda aka kashe Naira Biliyan 4.5 na kudin Korona a Jihar Kogi.
SERAP ta ce ya kamata gwamnan jihar Yahaya Bello ya fito ya yi bayanin yadda aka karkatar da kudaden. Shi dai gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa babu cutar kwata-kwata a jiharsa. Kungiyar dake fafutukar kare hakkin bil’adama da saka ido kan al’amuran kudi (SERAP) ta roki shugaba Buhari ya yi bincike kan yadda aka karkatar da wadannan kudade har Naira biliyan 4.5 na Korona.
Gwamnatin tarayya ta tura wa Gwamnatin Jihar Kogi Naira biliyan 4.5 da ta samu daga rance, da kuma gudummuwa da ta samu don yaki da cutar Korona, kamar yadda PM News ta ruwaito. SERAP ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Asabar. Ta roki Shugaba Buhari da ya ba wa Ministan shari’a da sauran hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa umarnin bincikar yadda aka kasafta kudin.
A jawabin SERAP ta ce: “Da zarar an sami kwakkwarar shaida, duk wanda ake zargi a hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata.” A jawabin Mataimakin shugaban kungiyar da Kolawole Oluwadare, yanya wa hannu ya bayyana cewa: “Ba da umarnin ga Ministan shari’a da kuma sauran hukumomin yaki da cin hanci doka ce a kundin tsarin mulkin kasar nan.” Kuma idan shugaba Buhari ya ba da wannan umarnin to yana kara tabbatar da bayanin da ya yi lokacin rantsar da shi “Zan tabbatar da duk wasu ayyuka an gudanar da su yadda ya kamata a dukkan matakan gwamnati” in ji Buhari.
Kungiyar ta ce ta damu da yawan korafe-korafe kan cin hanci da rashawa da kuma amfani da kudaden gwamnati ta inda bai kamata ba a dukkan jihohin Nijeriya. Daukar kwakkwaran mataki na yin bincike zai kara tabbatar da gaskiya da rikon amanar gwamnati wadda ta kunshi Jihar Kogi.
“Za mu yi matukar jin dadi idan aka dauki mataki akan korafinmu cikin kwanaki 14 da turo shi. Idan kuma ba a yi komai ba bayan wannan lokacin, SERAP za ta dauki matakin da doka ta tanadar wajen kalubalantar gwamnati har ta yi abin da ya dace.” Cewar SERAP. SERAP ta tura cikakken bayanin da ta yi a jawabinta zuwa ofishin Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shugaban ICPC, Professor Bolaji Owasanoye, da kuma shugaban Hukumar yaki da cin hanci ta kasa (EFCC) Abdulrasheed Bawa.