- Ya Ce, Da Gaske Ba Shi Da Lafiya
Daga Khalid Idris Doya,
Tsohon shugaban kwamitin farfado da tara kudaden fansho na kasa (PRTT), Abdulrasheed Maina, a jiya Laraba, ya sake rokon Alkalin babban kotun tarayya da ke Abuja, Justice Okon Abang, da ya bayar da belinsa.
Maina, a wata bukatar da ya gabatar mai kwanan wata 24 ga Disamba, 2020, da ke dauke da lamba kamar haka: FHC/ABJ/CR/258/19 ta hannun lauyansa, Anayo Adibe, ya shaida cewar, bukatar hakan ya zama dole ne lura da halin rashin lafiya da ke damunsa, wacce har batun ya kai ga tsananta.
Amma kotun ba ta zauna ba, domin sauraron wannan bukatar ba, inda ta dage shari’ar zuwa wani rana.
Kotun dai ta dage cigaba da sauraron shari’ar har zuwa 1 ga Fabrairun da ke tafe.
Shi dai Maina idan za ku iya tunawa a shekarar da ta gabata kotun ta taba bada belinsa kan miliyan 500 tare da gabatar da Sanatan da ke wakiltar Borno ta kudu, Ali Ndume a matsayin wanda ya tsaya masa wajen amsar belinsa.
Justice Abang, bayan jerin zaman da kotun ta yi ba tare da ganin Maina ba, ya sanya Alkalin soke izinin belin Maina din da ya bayar, tare da bada umarni mai karfi ga jami’an tsaro da su kamo shi a duk inda suka yi tozani da shi.
Lamarin da har ya kai ga kotun daure Sanata Ndume na ‘yan kwanaki sakamakon kaza kawo wanda ya tsaya masa a gaban kotu, kodayake daga baya kotun ta bada belin Ndume bisa nuna halin kwarai da biyayya da ya nuna, inda kotun ta ci gaba da shari’arta duk da babu Maina har zuwa lokacin da aka sake kamo shi gami da tuso kesarsa zuwa gaban kotun.
A dai ranar 4 ga watan Disamban 2020 ne EFCC ta sake kawo Maina gaban kotun bayan shafe wasu watanni da arce wa belinsa da aka bayar tun farko, domin cigaba da gurfanar da shi kan zarge-zargen da hukumar ke masa.