Mustapha Ibrahim Abdullahi" />

KA SAN JIKINKA: Sarauniyar Kirji

Tare da Mustapha Ibrahim Abdullahi 08037183735 musteeibr10@yahoo.com

Da akwai wata tsoka a farfajiyar kirji wadda ke harba jini duka sassan jiki, sannan kuma ta sarrafa tunani, ta saka ta warware kuma ta yanke shawara akan abubuwa da ke faruwa a rayuwar mutum.

Wannan tsoka itace zuciya. Ita ce gaba ta farko da ta fara aiki tun mutum yana ciki, dan saati uku. Kuma bincike ya nuna cewa ita ce ta karshen dena aiki idan rayuwar mutum ta kare.

Girman zuciya ya kai kwatankwacin dunkulen yatsun hannun ka ko hannun ki izuwa wuyan hannu. Tana da tsoka mai matukar karfi da kokarin harba jini zuwa kowacce kwayar halitta, ta hanyoyin jini manya, matsakaita da kanana.

Zuciya tana harba jini zuwa bangarori na jiki wanda yawan sa ya kai kimanin galan daya da kwata a duk minti daya. Sannan tana bugawa tsakanin sau sittin zuwa sau tamanin a duk minti daya; ya danganta da wasu dalilai, yanayi, ko halin da mutum yake ciki. Misali: zuciya ta fi bugawa da sauri yayin da kika ji tsoro, ko lokacin da kake wani aikin motsa jiki fiye da ace a zaune kake kana shakatawa. Wani misalin shine Zuciyar yaara tafi ta manya yawan bugawa a kowanne minti.

Ta kasance a cikin wata jaka da ake kira “pericardium”. Wannan jakar tana dauke da wani ruwa wanda yake taimakawa wajen rage tasirin gugar  da zuciya ke yiwa jakar, wato ruwan yana rage “friction” a turance.

A tsakiyar kirji zuciya take. A gaban zuciya, akwai kashi mai rike da kasusuwan hakarkari wanda a turance ake kira “sternum”. A bayanta, akwai bututun abinci wato “oesophagus”. Shi kuma a bayansa akwai kashin baya wato “bertebrae”

Shi yasa idan kaci ko kika ci abinci mai zafi kuma aka hadiye ba tare da ya huce ba, ake jin tsananin zafi yayin da abincin yazo tsakiyar kirji. Saboda Shi bututun abincin a jikin zuciya yake daga baya.

Zuciya ta kasance a tsakanin huhun hagu da na daama a kirji; kuma a zaune take akan wata shimfidaddiyar tsoka wadda ta raba kogon kirji wato “thorad” da kuma kogon kayan ciki wato “abdomen”.

Yanzu bara mu kalli kirar da Ubangijin halitta yayi wa zuciya. Daga waje, zaku ga dunkulalliyar tsoka ce kawai, amma daga ciki, tana da siffa ta dabam. Ta kasance tana da ta tsoka rubi uku: ta farko, wato ta waje ana ce mata “epicardium”. Ta biyu kuma, wato ta tsakiya ana ce mata “myocardium”. Wannan tsoka ita ce wadda rubinta ya fi na sauran kauri da karfi saboda ita ce ke da alhakin harba jini.

Ita kuma ta can ciki ana ce mata “ “endocardium”. Ita ce ta yi shimfida a cikin bangwayen zuciya na ciki, sannan daga bisani ta shiga cikin hanyoyin jinin da suka shigo zuciya; nan ma tayi musu shimfida.

Haka kuma, daga ciki, zuciya tana da hororo ko aljifai guda hudu: biyu a sama ( dama da hagu), biyu a kasa (dama da hagu). Da akwai shamaki tsakanin aljifan sama, na dama da hagu, kamar yadda akwai irin wannan shamaki a tsakanin aljifan kasa suma, dama da hagu.

Aljihun sama na dama, daga bayansa, yana da kofa guda biyu: daya a sama, daya a kasa. Ta saman ita ce kafar da jini daga saman jiki yake shigowa cikin zuciya. Ta kasan kuwa ita ce kafar da jini daga kasan jiki yake shigowa.

Haka kuma, a tsakanin aljihun sama da na kasa, bangaren daama, akwai kofa mai kamar bawul mai kula da shige da ficen jini. A can bangaren hagu ma, tsakanin aljihun sama da na kasa akwai irin wannan bawul mai kula da kai kawon jini.

Allah madaukaki yayi wa zuciya wata baiwa. Kamar yadda na dan gutsura muku cewa: duk wani motsi na jikin mutum, kwakwalwa ke kula da shi, da yarda da sanin kwakwalwa wannan gaba ke motsawa. Amma ita zuciya, kusan kishiyar hakan ne. Tana da abin da ake kira “autorhythmicity”, wato mai sarrafa kari na motsi da kanta.

Ta kasance tana da wata halitta mai kamar gujiya, wadda take a dab da karshen aljihun zuciya na sama na daama. Aikin ta shi ne samar da sakon lantarki da harba shi kasa  ta cikin wayarin din da ke jikin ta. Da zarar ta harbo sakon lantarki, akwai wata gujiyar kuma a tsakanin aljifan sama da na kasa, sai ta karbi sakon, sannan ita ma ta harba shi sauran rassa ko wayarin da ke jikin bangwayen zuciya na hagu da na daama. Idan hakan ta faru, to sai zuciya ta takura, ta harba jini.

Yanzu bara mu ga wasu kebance- kebancen wannan sarauniya dake tsakiyar kirjin bil adama.

Da akwai jijiyar motsi (nerbe), da ta taso daga kwakawalwa zuwa zuciya. A dabi’ance aikin ta shi ne rage saurin bugawar zuciya. Kunga kenan bugun zuciya “automatic” ne. A kaf tsokar jiki, zuciya kadai ke da wannan.

Ita kadai ce tsokar da a ko da yaushe cikin aiki take; ba dare ba rana, ba ruwan ta da bacci kake/ kike ko ido biyu, aiki kake ko hutawa, kawai aikin ta take kaddamarwa.

Babu tsoka mafi ‘Sakin hannu’ irin zuciya. Me yasa? Saboda kullum aiki take tukuru domin ta tabbatar cewa jini ya isa zuwa kowanne lungu da sako na cikin jiki. Abin da ya kamata mu gaane shine, kwayoyin halittar jiki ba jinin suke sha ba; a’a. Jini yana dauke da sindaran da suke bukata ne.

To bara na baku misali: kamar ace akwai wata unguwa, a cikin ta akwai hanyoyin kwata ko kwalbati. Kaddara jikin ka/ jikin ki shine unguwar, sannan kuma kwalbatin, shine hanyar jini. Sannan gidajen sune a matsayin kwayoyin halittar jiki. Idan kwata tana gudu, ai akan ji warin ta na tashi, harma ya shiga gidaje ko? To shin ana ganin warin?

To kamar haka suma sinadaran jiki suke yawo cikin kwalbatocin jini a jikin mu, suke bin iska su shiga cikin kwayoyin halittun mu. Idan sun amfana da sinaran (kwayoyin halittu), sai kuma dattin da suka tara shiga ya biyo iska ya shiga jini mai komawa izuwa zuciya domin a fitar dashi waje.

Sati mai zuwa, zan ci gaba in sha Allah.

Exit mobile version