Mustapha Ibrahim Abdullahi" />

Ka San Jikinka: Tsoka Mai Luwai-Luwai

08037183735  musteeibr10@yahoo.com

Yau, da yardar Mai kaga halitta, zan dan yi bayani akan wata tsoka da ake samun ta a gurare na musamman a jiki, wadda aikin ta, na da matukar muhimmanci a rayuwar mu; wannan ita ake cewa tsoka mai luwai-luwai.

Tsoka mai taushi ko ince mai luwai-luwai, ta sha ban-ban da tsokar nama da muka gama bayani akai, wato tsoka mai zane-zane, saboda irin kebantaccen aikin ta, da kuma bigiren ta: wato inda ake samun ta. Ana ce mata tsoka mai luwai-luwai ne saboda ba ta da zane-zane a jikin ta.

Wannan tsoka bata da kauri sosai, kuma ana samun ta ne a gurare masu hororo ko bututu, ta yanda abu zai iya wucewa ta ciki; misali bututun abinci, tun daga makogwaro har zuwa dubura. Wato su tumbi, uwar hanji, da karamin hanji.

Hanyoyin jini suna da bangon ciki da kuma na waje. Bangon ciki, na hanyoyin jini shi ma yana dauke da wannan tsoka mai luwai-luwai. Tana taimakawa wajen tabewa yayin da jini zai wuce ta cikin su, da kuma shikawa bayan jinin ya wuce.

A na kuma samun wannan tsoka a bututun iska ( hanyoyin da iska ke bi yayin numfashi), da kuma bututu ko hanyoyin da muke biyan bukatun mu na mutuntaka.

A idanun mu ma akwai wannan tsoka inda aikin ta shi ne kula da tsukewa da walawar kwayar ido. Misalin yadda zaku gaane tsukewa da budewar kwayar ido shine: mu dauka a misali ka dade a zaune a waje mai duhu, ko ba wuta.

Ya zakaji idan ace wani yaazo kwatsam ya dallare maka ido da sabuwar tocilan, ko kuma ace kwan lantarki na saitin idon ka baka sani ba, sai aka kawo wuta? Ya zaka ji a cikin idon ka?

Ina zaton ai hakan zai sa ka rufe idanun ka. To a wannan lokacin da haske ya dallare maka ido, sai tsoka mai luwai-luwai da ta kewaye kwayar idon ka ta tsuke. Yayi da kuma ka saaba da hasken ko kuma ka fita ka shiga cikin duhu, sai kwayar idon ta shika. A lokacin da mutum yaji firgici shima wannan tsoka ta cikin kwayar ido tana shikawa ta kara girma.

Ita ma faatar jikin mu tana da wannan tsoka daga ciki. Yayin da mutum ya tsorata, tsokar sai ta taakura, daga nan kuma gashin da yake jikin fata sai ya mimmike a sanadiyyar takurewar tsokar.

Haka nan kuma ana samun wannan tsoka a bangon mafitsara da kuma bangon mahaifa. To shin wane irin aiki suke gudaanarwa a wadannan wurare.

Na farko dai ita wannan tsoka tana bawa mafitsara (urinary bladder) daamar ajiye fitsari zuwa wani lokaci kafin a fitar da shi. To idan fitsari na taruwa, ita kuma tsokar tana kara budewa da tabewa domin ta saamar da isasshen waje ga fitsarin da ke taruwa.

Idan babu wannan tsoka, to fa da zarar fitsari ya cika mafitsara, babu damar jinkiri ko ajiye shi zuwa wani lokaci. Bayan mutum ya fitar da shi, sai mafitsaarar ta koma asalin yadda take da.

Abin da ke faruwa a mahaifa ma kusan hakane. Tsoka mai taushi da take cikin bangon mahaifa tana budewa da tabewa domin ta saamar da isasshen waje ga dan taayin da yake girma a cikin ta. Kun ga ashe tsokai mai luwai-luwai tana taka muhimmiyar raya a rayuwar dan adam.

A takaicce dai ita wannan tsoka ana samun ta a guraren da suke bada damar fitar wani abu daga jikin mu. Kunga bukatun mutuntaka kamar hutu, bayan gari, bawali, atishawa, fitar hawaye, haihuwa, da inzali da makamantan su, hanyoyin da suke biyowa na dauke da wannan tsoka.

Wannan tsoka tana motsawa ne ba tare da yardar mu, ko nufin mu ba, wato “inboluntary muscle” a turance. Idan kin ci abinci, baki da damar motsa tsoka mai taushi dake makokwaron ki domin ta tura abinci izuwa tumbi.

Haka kuma idan tumbin ka yana gauraya abinci, ta hanyar shikawa ta tabewar wannan tsoka mai luwai-luwai, to baka da ikon dakatar da tsokar, ko kace baka shirya ba.

Exit mobile version