Connect with us

MAKALAR YAU

Kabilanci Da Son Kai Sun Kassara Mu

Published

on

Son kai (musamman na rashin adalci) shine ginshikin da ya janyo rushewar dimbin dauloli da su ka shude a baya. Duk al’ummar da ta yi watsi da adalci tsakanin yayanta, sannu a hankali wannan al’umma za ta fuskanci zaizayewar karfinta har ta kai ga rushewa. Amma kash! Abin takaici shine cewa duk da kasancewar yadda tarihi ya bar mana hujjoji na hadarin kabilanci da son kai da yadda ya ke kassara zamantakewa, al’ummomi da dama sun kasa wa’aztuwa. Ban san wata kasa wadda a ka gina ta a kan tubalin son kai da bangaranci irin kasa ta Nijeriya ba. Domin a shekarar 1914 lokacin da turawan mulkin mallaka su ka hade mabanbantan yankunan arewaci da kudancin Najeriya, babu wani abu guda wanda su ke kan daidaito idan ban da cewa dukkanmu yan afirka ne bakake.

Daular Usmanu Danfodiyo, wanda ta faro daga gefen Hamada ta ratsa har zuwa duwatsun mambila sannan daga gabobin tafkin Chadi har tsallaken kogunan kwara da na binuwai sun fado cikin wannan daula ta shehu. Amma saboda hadama irin ta turawa, maimakon su bar wannan yankin a matsayin kasa guda sai su ka hade shi da yankin kudancin Najeriya saboda dalilai na bukatarsu ta tattalin arziki. Da farko dai yankin daular shehu na da cikakken tsari na mulki da zamantakewa wanda ke kafada-da-kafada da na uwargijiyarta wato Daular Birtaniya, shi ya sa ta hade yankunan biyu yadda za su sami damar tatsar arzikin noma da ke arewa zuwa teku a Lagos domin haurewa da shi kasar Ingila. Sakamakon arewa ta fi kudanci ingancin tsarin mulki, sai turawa su ka yanke shawarar ganin cewa yan arewa sun mamaye yadda za’a mulki Najeriya a nan gaba.

Shugabannin farko na arewa sun iso dandalin mulki cike da karsashin wannan banbanci tsakanin kudu da arewa musamman sanin cewa sune yayann Mowa a wajen turawa, yayin da ‘yan kudu ke cike da jin haushin arewacin kasar ganin sun dara su a kan ilimin boko. Ba abin mamaki ba ne kasancewar jerin yan boko na farko a arewa, duk sun fito daga manyan gidaje ne, saboda masaniyar cewa su ne za su ci gaba da rike kasar ko da turawa sun tafi, don haka ‘yayan manya kawai, musamman sarakuna da na kusa da su, sune su ka sami wannan dama. Abin takaici kuma sai su ka dora kasar gaba dayanta kan tsarin “wa ka sani, ba me ka sani ba”. Wannan kuma shi ya saka harsashin durkushewar mu domin duk wadanda ke kan madafan iko na kokarin cika aljifansu ba tare da tunanin ya al’umma za ta kasance ba. Wannan ginshiki shi ne ya haifar da salwantar mutuwar mutane sama da miliyan daya sakamakon yakin basasa da ya barke bayan Inyamurai sun kashe su Sardauna sannan yan Arewa su ka kashe Ironsi a wani juyin mulkin na ramako.

Tun daga wancan lokaci sai kowanne yanki a kasar ya dukufa wajen ganin cewa ya cusa nasa a bangarorin mulki da aiwatar da gwamnati ba tare da la’akari da cancanta ta kwarewa ba. A arewa su Sardauna sun ci gaba da gina wannan dabi’a yadda bayan kaucewarsu sai wadanda su ka gaje su, su ka tsunduma cikin cin hanci da rashawa, abinda ya durkusar da duk wani yunkuri na kawo ci gaba. Kabilanci, son kai da cin hanci da rashawa sun zama abubuwa da su ka kassara kasar Najeriya musamman arewaci. Duk da cewa Sardauna ya yi yunkuri wajen kawo ci gaba a arewa amma wancan tsari na son kai da zabar wasu sama da wasu ya hana magadansa su iya kawo canjin da aka yi fata. Shi kuma gidan da aka gina da tubalin toka sunansa rusashshe.

Tun daga samun yan cin kai, ba wata gwamnati wadda ba’a zarge ta da nuna son kai wajen raba mukamai ba, kuma akwai gaskiya cikin zargin. Kwanan nan Dangiwa Umar ya zargi gwamnatin Buhari da nuna banbanci wajen raba mukamai, amma ya manta cewa mutane irinsa da mai gidansa (IBB) na daga cikin wadanda su ka dada tabbatar da wannan dabi’a a cikin sha’anin mulki. Dan gidan sarautar Gwandun, ya na karamin soja (manjo) Babangida ya dauko shi ya ba shi gwamnan jihar Kaduna a lokacin da duk manyan sojojin arewa ke Kaduna, kuma akwai janarori da dama cikinsu.

Mun wayi gari bama ganin cewa nuna son kai irin wannan ba wani abu ba ne domin sai ka ji labarin yadda Sardauna ya yi hakan kuma ana dauka abin burgewa ne ba tare da masaniyar cewa abin da zai kassara mu kenan ba. Duk al’ummar da ta ce son kai ne a’ala hakika zaka tarar ta ginu bisa zalunci, kuma matukar ba’a tattaru an yaki son kai ba hakika sai ya murkushe wannan al’umma.

Na yi zaton cewa wannan annoba ta kwarona za ta sa shugabanninmu su wa’aztu su gane cewa adalci ne mafita, musamman idan ka yi la’akari da mutuwar Abba Kyari wanda a yan makonni da su ka gabata ya kasance wanda ke da karfin iko da ake ganin kamar ma shine shugaban kasa, domin hatta ministoci an ce sai ya sahale musu za su iya saduwa da shugaban kasa. Amma ya na mutuwa, cikin makonni kalilan har an manta da shi kuma hatta abubuwan da ya zartar a lokacin ya na raye, an wayi gari shugaban kasa ya soke wasu.

Wannan annoba ba ta yi wa mahukunta wa’azin da na ke zato ba, domin a cikin gayararren kasafin kudin da shugaban kasa ya sake mikawa majalisa domin su sahale masa, sai ga shi a cikin kudi biliyan 37 da aka saka domin gyaran ginin majalisa an rage shi zuwa biliyan 27 (wato kashi 25%) amma kuma kudade biliyan 69.9 da aka ware domin matakin lafiya na farko an zaftare shi zuwa biliyan 25 kacal (wato kasha 42.5%) kuma a lokacin da ake cikin tsaka da annobar kwarona. Shi ma kudaden hukumar ilimin bai daya ta kasa an rage shi daga biliyan 111.7 zuwa biliyan 51  (wato fiye da rabi 54.2%). Idan  muka kalli jumlatan kasafin kudin majalisun tarayya guda biyu mai wakilai 463, an ware musu naira biliyan 139 yayin da a daya bangaren idan ka hade kasafin kudin ma’aikatar lafiya da ta Ilimi (da aka tanada domin mutane miliyan 202) naira biliyan 94 kawai.

Tsarin daukar aiki wanda ke la’akari da yanki da ka fito (Federal character) da kuma tsarin bada mukamai na siyasa das hi ma ke dogaro da yankinka, dukkansu sun dada saka nakasu da fifita bangaranci da son kai a kasar. A lokacin Abacha yawancin masu rike da mukaman tsaro yan Kano ne, haka lokacin Obasanjo, Yar’Adua, Jonathan da Buhari duk za ka samu manyan mukamai na nuna daga wane bangare shugaban kasa ya fito. Ba ka iya fahimtar haka a yanzu sai ka dubi jerin wadanda ke rike da mukamai a kamfanin mai na kasa (NNPC) domin shugaban hukumar, shugaban kasuwanci, shugaban ayyukan kamfanin, shugaban sashen fetur da gas, Sakatare kuma shugaban lauyoyi, shugaban tace mai, shugaban harkar makamashi, shugaban sabbin makamashi, shugaban kula da asara, Shugaban Fito, shugaban matatar Port Harcourt, Shugaban harkar lafiya, shugaban kasuwancin gas, shugaban saka jari a harkar gas da makamashi, shugaban kasuwanci da shugabannin kamfanonin NAPIMS, DPR, NPDC da DUKE OIL, dukkansu yan arewacin Najeriya ne.

Babban abin takaicin ga arewa shine, kamar yadda Mathew Kukah ya fada a wata mukalarsa cewa “Gara barawon kudu da barawon arewa” shine yawancin yan arewa da su ka kai tsaiko a harkokinsu na rayuwa, musamman na gwamnati wadanda ko ba’a fada maka ba ka san cewa dukiyar da su ka tara ba tsabar hakkokin albashinsu ba ne kawai, amma ba za ka samu su na iya tallafawa talakawan da ke cikin iyalinsu ba ballantana na garuruwansu ko kauyukansu.

Cikin wadancan mutane na san wasu guda biyu amma na san cewa ba sa iya tallafawa yan uwansu talakawa da kudin makarantar yayansu ballantana su yi gidauniyar tallafawa ilimi. Wani ma ya siyawa kanin matarsa gida a Abujaamma bai iya siyawa dan yayansa da ke aiki a Abuja motar hawa ba sai dai ya hau tasi zuwa ofis.

Saboda damar da irin wadannan manya na arewa su ka samu ba sa tunanin ni’ima ce ko kuma akwai hakkin al’umma a kansu ko kuma Allah zai tambayi kowacce irin ni’ima yadda ka aiwatar da ita domin shi bai taba baka wata ni’ima don karan kanka da iyalinka kawai ba. Amma a kudu ba haka abin ya ke ba, dole duk abinda ka ke da shi ka samma al’ummarka ta hanyoyin tallafin karatu, gina makaranta ko koyawa yara irin sana’ar da kake yi. Amma yan arewa “Ramin kura ce daga su sai yayansu”

A wannan makon na karanta wani labari na wani basarake a kasar yarbawa wanda ya kirkiri wata makarantar kwana ya ke daukar nauyinta domin ‘ya’yan talakawa wadanda iyayensu ba za su iya biya musu kudin zuwa kowacce irin makaranta ba. Ana basu wajen kwana, abinci, littafai, kayan makaranta har da kwamfuta da yanar gizo duk a kyauta kuma basaraken na cikin malaman da ke koyarwa a wannan makaranta.

Wannan ya sa na tuna da tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, wanda na san ya fi wancan basarake kudi amma ban san wata makaranta da ya gina ko tallafin karatu da ya ke bayarwa ba. Dangote da Abdussamad na cikin fitattun masu arziki a Afirka amma ban taba jin jami’arsu ba, ko kuma gidauniyar ilimi ko tallafin masu sabuwar sana’a wanda ake yi duk shekara (wannan ya tuna min da kaninsu a jerin biloniyoyin Najeriya, wato Tony Emelu da ke bada irin wannan tallafi duk shekara). A yanzu ana ta kiran a soke almajiranci, kuma ba tare da wani tsari na tallafa musu ba, shin wannan zai haifar da da mai ido kuwa? A wannan lokaci da sana’a mafi ci a arewacin Najeriya ita ce satar mutane da ta’addanci?

Bangaren malaman boko sun taimaka wajen murkushe ilimi domin an yi watsi da bincike an dora boko a matsayin hanyar samun takardar shaida domin samun aiki kawai. Bincike ya mutu murus a jami’o’in mu duk da katafariyar jami’ar Ahmadu Bello, wato babbar sadaukarwa da Sardauna ya yi wa arewa kenan domin assasa noma, wanda da an dora daga wancan lokacin da yanzu muna iya ciyar da Afirka gabadaya.

Amma an wayi gari tsarin binciken harkar noma ya mace yadda dama-damai da koramun da muke da su a arewa su na nan zaune ba mamora, a kasar da ke siyo kifi daga waje na kimanin naira biliyan dari hudu duk shekara. Najeriya ce kasa mafi karfin tattalin arziki a fadin Afirka amma kuma ita ce ke da mafi yawan matalauta a duniya (kaso 15% na yawan matalauta a duniya kimanin mutane miliyan 102), kuma akasarin wadannan matalauta su sun fito daga yankin arewacin Najeriya ne. Raba arzikin kasa shi ne maganin wannan yanayi amma ba zai yiwu ba sai an yi watsi da bangaranci, son kai da cin hanci, a dawo da cancanta kawai ba tare da la’akari da wanda ka sani ba. Ko dai mu hadu gabadaya mu yi wannan yakin ko kuma yakin ya cinye mu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: