Tun farko, al’ummar Luba na da adanannun al’adunsu na rayuwa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka yankin. Baya ga kwarewar da suka yi a harkar sassaka itatuwa da gina tukwane da sauransu, al’ummar na kuma cin arzikin ma’adinan karkarshen kasa muasamman karfe, wadanda Allah ya azurta yankin da su. Ganin irin nasarorin da yankin nasu ya samu hada da kurmi gami da tsaunukan da suke da su a tsibirinsu, hakan ya ja hankalin ‘yan kasuwa da mahara da kuma yake-yake a tsakiyar karni na goma sha tara.
Fannin ilimin nazarin al’adun mutanen da suka gabata na da ra’ayin cewa, jama’ar Luba sun fi sabawa da zama a kauyuka da ke kusa da bakin koguna a lardin Upemba. Tun asali tsarin gidajensu ba na ginin kasa ba ne, suna amfani ne da bukkokin da suke hadawa ta hanyar amfani da itatuwa, ko ganyayyaki da ciyayi, ko kuma wasu ma’adinai da suke da su a yankin. Wani abin tausayi shi ne, ‘yan kabilar kan shiga halin ni’yasu a yankin a sakamakon yadda a wasu lokutan sukan yi fama da ambaliyar ruwa ta dalilin cika da batsewa da koguna kan yi musamman idan damina ta tsala.
Dangane da fasaha da yanayin tattalin arzkin da suke rayuwa a kai kuwa, wani masanin tarihi Farfessa Thomas Reefe, ya bayyana cewa al’ummar Luba sun kware wajen hako ma’adinan karfe tare da sarrafa su zuwa abubuwan amfanin rayuwa kamar su sarkar wuya, kugiyar kamun kifi, masilla da dai sauransu.
Masarautarsu
Kamar yadda ya zo a tarihi na baka (ba a rubuce ba), akwai sarakuna biyu da ke mulkar Luba tun kafin karni na 16, su ne: Sarki Nkongolo Mwamba wanda ya kasance shaidanin Sarki da kuma Sarki Mbidi Kiluwe wanda ya kasance mutum adili. A lokaci guda ake nada sarakunan biyu a kan gadon mulki. Game da Sarki Nkongolo, shi tantirin tsohon najadu ne, domin kuwa shaye-shaye, yi wa mata fyade, kwace dukiyoyin jama’a da sauran munanan dabi’u babu wanda ya bari. Yayin da Sarki Mbidi Kiluwe ya kasance akasin haka, mutum ne mai nagarta da dattako, ga tausayi da kwatanta adalci a harkokinsa. A tarihi, Sarki Nkongolo ya zama suriki ga Sarki Mbidi, sakamakon Mbidi na auren wata ‘yar’uwasa inda suka samu haihuwar wani yaro mai suna Kalala. Al’amarin da ya cusa wa Sarki Nkongolo kishi da hasada har ya kai ga kitsa yadda zai hallaka Kalala dan Sarki Mbidi, saboda yadda yaron ya gaji ubansa cikin halayyar kirki da kuma kin munanan halayen kawun nasa. Sai dai, Kalala ya samu kariyar abin bautarsu daga sharrin kawun nasa.
Addinin gargajiyar al’ummar Luba, ya kunshi yin Imani da dodon da suke bauta mai suna Shakapanga da kuma Leza, lamarin da ke nuna su ne manyan ababen bauta da suka kebanta da gargajiyarsu. Haka nan, a tsarin addinin nasu, sun yi ammanar cewa abu ne mai yiwuwa samun zantawa tsakanin wadanda ke raye da kuma matattunsu. Bugu-da-kari, tsarin addinin jama’ar Luba, ya hada da gabatar da addu’o’i, raye-raye da wake-wake, bayar da sadaka da sauran ‘yan tsafe-tsafen da ba a rasa ba. Kazalika, lamarin addinin nasu har way au, ya kunshi kyakkyawar mu’amala da juna, girmama juna da makamantansu.
Kamar yadda tsarin zamantakewar al’ummar Luba ya nuna, sun fi sha’awar zama tare inda tsarin gine-ginensu ya fi kama da bukka ko makamancin haka. Mutane ne masu farauta da su (kamun kifi) a kogunan da ke kewaye da su. Haka ma ta fannin amfanin gona irin su rogo, masara, ‘ya’yan itatuwa har ma da kiwon dabbobi, duk ba a bar su baya ba. Sai kuma sana’ar sassaka da gina tukwane.