Connect with us

TARIHI

Kabilar Ma’asai: Dalilin Shan Jini Da Kiwon Shanu

Published

on

Ma’asinta shi ne a ke dauka Uba kuma wanda ya samar da tsatson kabilar Maasai, ance ya samu kyautar shanu ne daga Ngai – Ubangijin sama- wanda ya sauko da shanun daga sama zuwa kasa acikin salkar fata.

Tun daga wannan lokacin suke kallon shanu a matsayin tsarkakku,  kuma darajar su tana kaiwa kafada da kafada data ‘ya’yansu. Hakika yawan yara da yawan shanu ke nuni da tumbatsar mutumin kabilar Maasai.

Dajin da ya ratsa shahararrun yankunan Ngorongoro, Amboseli, Serengeti, Masai Mara da Tsabo dukkan su nan ne wuraren kiwon alummar Maasai. Kabilar Maasai na amfani da yaren Maa ne, kuma ana samun su a yankunan kasashen Kenya da Tanzania.

Haka Kuma duk da yadda sauyin zamani ke tunkude al’adu ga kabilun duniya, amma kabilar Maasai suna yaki tukuru wajen kere al’adun su na kaka da kakanni, don haka suka yi shura a cikin kabilun kudancin Afirka musamman wajen kiwon shanun su, tafiya bisa tituna ko rawar adumu.

Daga cikin shahararrun al’adun gargajiya na kabilar Maasai akwai rawar tsalle ta adumu, sanya tufar ‘shuka’ mai kaloli, da yin kaki ko kuma kwankwadar jini.

Adamu shine sunan rawar tsalle-tsalle da akeyi a matsayin biki yayin da yara matasa suka zama mahankalta wadanda suka isa aure. Ana rera wakoki  nangargajiya yayin bikin, sannan wanda tsallen sa yafi na kowa shine yayi nasara, kuma shi ke samun macen aure da tafi ta saura.

Kalar tufafin shuka da su ka fi sanyawa itace Ja, wadda ta ke wakiltar jini, kuma take a matsayin kariya a garesu ga namun daji. Yayin da shudiya ke nufin sararin sama wadda ke samar da ruwan sama ga shanu. Kalar rawaya kuwa na nufin haihuwa da girma. Baki dayan wadannan tufafi na su ke kara musu keɓantaka a cikin kabilun afirka.

Kasancewar a cikin wasu kabilun ana kyamar kaki, amma a Maasai shi abin so ne, domin babban abin girmamawa ne idan zaka gaisa da mutumin da kake girmamawa sai kayi kaki ka tofa a tafin hannu sannan ka mika masa hannun ku gaisa. Hakan na nufin share dukkan wani sharri daga tafin hannun, haka kuma idan kaje barka sai ka tofa kakin ka a goshin yaron sannan ka nuna soyayyar ka a gare shi. Shan jini kuwa wani abu ne da ya zama ruwan dare a gare su.

Don haka alummar kabilar Maasai na shan jini ne a matsayin sinadarin kara lafiya da kuzari. Jinin da suka fi sha kuwa shine na saniya, wanda har sukan gauraya shi da madara su kwankwada abinsu a duk sanda suke so.

Zuwa yanzu kabilar ta rarrabu zuwa 21 kamar haka, kuma kowacce na da dan sirkin al’adu da saura:- Keekonyokie, Damat, Purko, Wuasinkishu, Siria, Laitayiok, Loitai, Kisonko, Matapato, Dalalekutuk, Loodokolani, Kaputiei, Moitanik, Ilkirasha, Samburu, Lchamus, Laikipia, Loitokitoki, Larusa, Salei, Sirinket da Parakuyo.
Advertisement

labarai