Tasallah Yuan Ta CRI Hausa" />

Kada A Shafa Wa Xinjiang Kashin Kaji Kan Wadatuwarta Da Ci Gabanta

A ranar Laraba 25 ga wata, rana ce ta cika shekaru 70 da ’yantar da jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashinta ta kasar Sin cikin lumana. Sakamakon tsawon shekaru da aka kwashe ana raya jihar, ya sa jihar ta Xinjiang ta zama kofar kasar Sin da ke arewa maso yammacin kasar, a maimakon yankin karkara da ya taba fama da koma-bayan.
A shekarun baya, matakan da ake dauka a jihar Xinjiang wajen yaki da ta’addanci, da kau da tsattsauran ra’ayi, sun dawo da kwanciyar hankali a jihar, wadda ta shiga sabon lokaci na samun wadata da ci gaba.
Amma wasu kasashen yammacin duniya sun kulla mummunar makarkashiya, suna ta soke-soke da bata sunan jihar ta Xinjiang, tare da shafa wa kasar Sin kashin kaji a tarurrukan kasa da kasa.

Dangane da matakan nasu, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana ra’ayin kasar Sin a jiya Talata 24 ga wata, a yayin wata liyafar da aka shirya a birnin New York na Amurka, inda ya yi nuni da cewa, matakan da jihar ta Xinjiang take dauka bisa doka, na yin rigakafin abkuwar hare-haren ta’addanci, sun dace da dokokin kasar Sin, sa’an nan sun cancanci tunanin kasashen duniya. Ya ce ta dalilin hakan, ba za a samu nasarar kitsa wa Xinjiang sharri da kuma bata sunanta ba.
Jihar ta Xinjiang dai ta samu manyan nasarori cikin shekaru 70 da suka wuce, ta kuma kasance wani abin misali ne a kasar Sin a fannin raya yankunan da aka fi samun kananan kabilu, lamarin da babu wanda zai iya musunta shi, kuma dukkan bakin da suka taba ziyartar sa, sun amince da hakan.
Wadanda suke kin jinin kasar Sin cikin kasashen yammacin duniya, ba za su samu nasarar matsa wa kasar Sin lamba bisa hujjar Xinjiang ba, kuma ba za su iya musunta ci gaban Xinjiang bisa karyarsu ba.

Exit mobile version