Muhammad Awwal Umar" />

Kada Ku Bari A Yi Amfani Da Ku – Hon. Abdurrahman Ga Matasa

An nemi matasan karamar hukumar Bosso da su daina barin ana amfani da su akan abubuwan da za su kawo wa Nijeriya matsala.

Shugaban majalisar kansulolin karamar hukumar Bosso ta jihar Neja, Hon. Abdurrasheed Abdurrahman ne yayi kiran lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a sakatariyar karamar hukumar da ke Maikunkele.
Hon. Abdurrasheed, ya cigaba da cewar saboda ganin cewar gwamnati ba ta iya baiwa kowa aiki yasa ta mayar da hankalinta wajen bunkasa kananan sana’o’in hannu da noma dan anfani matasa, wanda dukkanin bangarorin anfani gona ba a bar su a baya ba.
Ya kamata matasa su fahimci wannan kusurin na gwamnati hanya ce ta bullo da shi dan inganta rayuwarsu, wanda duk matashin da ya rungumi wannan kudurin zai kaucewa zaman kashe wando wanda wasu ke anfani da shi wajen daukar dawainiyarsu akan ayyukan da ba su da ce ba.
Maigirma gwamnan Neja na kokarinsa wanda shugaban karamar hukumar mu ta Bosso, Hon. Abubakar Suleiman Gomna a tsaye ya ke wajen ganin matasan karamar hukumar nan sun anfana, yadda gwamnatin karamar hukuma ke kokarin ta, muddin matasan mu za su bada goyon baya ina kyautata zaton batun rashin aikin yi ga matasan karamar hukumar nan zai zamo tarihi nan ba da jimawa ba.
Ya kamata ‘yan siyasa da sauran shugabanni su dage da fadakar da matasa muhimmancin dogaro da kai, wanda shi kudurin wannan gwamnatin na mu, yanzu haka maganar kananan sana’o’in hannu dan matasa shugaban karamar hukuma na kokarinsa wajen hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin gwamnati wadanda ke da alhakin horar da matasa sana’o’in hannu daban daban ta yadda kowa zai iya dogaro da kan shi.
bangaren noma kuwa, shirin babban bakin Najeriya ( CBN) da gwamnatin jiha, mun rungume shi hannu biyu ta yadda kananan manoma za su anfana.
Hon. Abdurrasheed yace yanzu haka saboda kudurin kyautata rayuwar al’ummar karamar hukumar nan, duk da halin rashin kudi da gwamnati ke fama da shi saboda matsalar tattalin arzikin kasa da ake fuskanta shugaban karamar hukuma da majalisar kansulolin mu mun himmantu wajen gyara motar noma da ta lalace da taraktocin gyaran hanya mallakin karamar hukuma wanda na tabbatar dawo da su zai taimaka wajen gyaran hanyoyin karkara da samar da tsaftataccen ruwan sha.
Saboda haka ina jawo hankalin jama’ar karamar hukumar Bosso kamar yadda su ka ba da amanna wajen zabo dan wakiltar su a karamar hukumar nan, idan su ka cigaba da ba mu goyon baya da addu’o’in alheri ina da tabbacin za su yi alfahari da zabin jam’iyyar APC a shugabancin karamar hukumar nan da Neja baki daya.
Ina kira ga ‘yan uwana matasa da su sani cewar kudurce kudurcen gwamnatin nan na cigaban kasa da zai inganta rayuwar su ta hanyar shugabancin adalci da jagoranci na gari.

Exit mobile version