Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya shiga tsakani a takaddamar da ake tsakanin Matatar Dangote da Kungiyar Ma’aikatan Mai da Gas (PENGASSAN), inda ya roƙi ɓangarorin biyu da su yi hakuri, su kuma nuna kishin ƙasa, da amfani da tattaunawa wajen warware rikicin.
Shettima ya gargadi ma’aikata da kada su ɗauki matakin da zai iya durkusar da ƙoƙarin masana’antar Dangote, wadda ya bayyana a matsayin babbar nasara a tattalin arzikin ƙasa. A cewarsa, ana iya magance matsalar cikin sauƙi idan aka zauna teburin tattaunawa.
- PENGASSAN Ta Yi Watsi Da Tayin Dangote Na Biyan Ma’aikata Albashin Shekaru 5 Ba Tare Da Yin Aiki Ba
- PENGASSAN Ta Musanta Janyewa Daga Yajin Aiki, Ta Gargaɗi Dangote
Yayin da yake jawabi a lokacin taron tattalin arzikin Nijeriya na 31 (NES_31) a Abuja, Shettima ya bayyana Alhaji Aliko Dangote a matsayin “ba kawai mutum guda ba ne, amma yana matsayin cibiyar tattalin arziki,” yana mai jaddada cewa dukkan ‘yan Nijeriya ya kamata su kare wannan jarin da ya zama ginshiƙi ga tattalin arzikin ƙasa.
“Dangote ba mutum ne kawai ba; wata cibiyar tattalin arziki ce. Ya zuba jarin dala biliyan 10 a Nijeriya maimakon ya kai kasashen waje. Idan ya saka hannun jari a Microsoft ko Amazon, da ya fi biliyan 70 a yau. Saboda haka, dole ne mu kare wannan jarin da ya zuba,” in ji shi.
Shettima ya bukaci dukan ɓangarorin da su yi amfani da hankali da kishin ƙasa wajen warware rikicin, yana mai cewa rigingimu na masana’antu ba su kamata su hana ci gaban tattalin arzikin ƙasa ba.
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa.
A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman mafita a abubuwa da yawa, ya zama dole ne mu haɗa kai wajen kare abin da ke amfanar ƙasa baki ɗaya.”