An Kaddamar Da Hedikwatar ‘Yan Sanda A Garin Lafiya

Daga  Zubairu T. M. Lawal, da Abubakar Abdullahi, lafiya

Sufeto Janar na rundunar ‘yan sandan kasa Ibrahim Kpotun Idris, ya kaddamar da sabuwar shalkwatar rundunar ‘yansanda da gwamnatin Jihar Nasarawa ta gina a garin Lafiya babban birnin jihar tare da mika ginin kyauta ga rundunar a matsayin gudummowa domin karfafa mata gwiwa game da harkokin tsaro a fakin jihar.

Da yake kaddamar da ginin, Sufeto Janar Idris ya ce gina sabuwar shalkwatar da kyautar da ita ga rundunar ‘yansanda zai taimaka gaya wajen inganta harkokin jami’an rundunar a jihar.

Dagan an saiya bayyana godiyar rundunar ga gwamnatin Jihar Nasarawa a kan yadda ta gano kaya daga cikin muhimman bukatun rundunar ta kuma samar da ita, tare da yin kira ga kaukacin jama’a da a bai wa ‘yansandan hakin kan da suke bukata a kowane lokaci domin ba su dama ci gaba da inganta sha’anin tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma baki kaya.

Bugu-da-kari, Sufeton ya bukaci kaikaikun mutane da kamfanoni da Allah ya hore musu da su yi koyi da abin da gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi na agaza wa ‘yansanda domin karfafa musu gwiwa.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce, gwamnatin jihar ta gina da kuma mika ginin shalkwatar kyauta ne saboda irin muhinmancin da aikin tsaro ke da shi ga rayuwar al’umma da kuma samar da kyakkyawar yanayin yin aiki ga jami’an ‘yansanda a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin sake dawo da tsarin sintirin jami’an ‘yansanda na Operation Nasara domin samar da wani kwamitin binciko muggan ayyuka a ko’ina a fakin jihar.

Daga nan, sai ya shawarci rundunar ‘yan sanda ta kasa da ta inganta matakan da ake bi wajen shiga aikin kan sanda sannan a tabbattar da cewa ‘yansanda suna samun dukkanin kayayyakin aikin da suke bukata.

Tun da farko, da yake tofa albarkacin bakinsa, kwamishinan ‘yansanda jihar Abubakar Sadik Bello ya bayyana cewa, kaddamar da sabuwar hedkwatar rundunar ya buke wani sabon babi a kudin tarihin ‘yansanda Nijeriya.

Da yake bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu a jihar, kwamishina Bello ya ce rundunar ta yi nasarar cafke wakanda suka aikata manya laifuka su 328 haka da manya da kananan makamai da dama.

Ya kuma bayyana matsalolin da ke ci wa rundunar tuwo a kwarya a jihar da suka haka da karancin jami’ai da karancin motocin sintiri da sauransu wanda a cewarsa, hakan na haifar wa rundunar cikas a harkokinta.

Exit mobile version