An Kaddamar Da Jirgin Ethopia A Kaduna

Jirgin musamman na Ethopia Airline ya tashi daga jihar Kaduna zuwa Adis Ababa da sauran kasashen duniya,don fara jigila daga kasa zuwa kasa.Idan za a iya tunawa dai Ethopia Airline shi kadai ne jirgin da ke zuwa kasashen duniya da ke sauka a filin jirgin saman Nmandi Azikiwe da ke Kaduna lokacin da aka kwashe tsawon mako shida ana gyaran filin.

A lokacin da yake jawabi wajen bikin tashin jirginna farko, bayan kammala aikin filin jirgin karamin ministan kula da filayen jiragen sama Sanata Hadi Sirika, ya tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na bayar da cikakken goyon baya a harkar sifirin jiragen sama. Saboda haka, sai ya yi kira ga sauran kamfanoni jiragen sama na kasashen Afirka da su kulla dangantaka da filin jirgin na Kaduna.

Shi ma da yake nasa jawabin shugaban Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, InjiniyaSaleh Dunoma, ya bayyana cewa, sauka da tashin jiragen sama abu ne mai matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, saboda haka, al’ummar jihar Kaduna za su amfana da wannan filin jirgin sama matuka, sannan su ma Hukumarsu za ta samu kudaden shiga wanda za su taimaka mata wajen ci gaba  dakula da filin jirgin.

Injiniya saleh ya ci gaba da cewa, fara  jigilar zuwa kasashen duniya da jirgin Ethopia Airline ya yi kamar wani mabudi ga nsauran kamfanonin jiragen sama na duniya, domin yawan fasinjoji zai karu, wanda kuma zai sa sauran kamfanonin jiragen sama na duniya, su shigo a dama da su.Saboda haka, ya ce, za su bayar da cikakken goyon baya ga dukkan  kamfanin da ya zo na ganin ya samu nasara.

Shi kuwa, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i, nuna farin cikinsa ya yi musamman da aka samu wannan nasara lokacin mulkinsa. Yace, jihar Kaduana ta dade tana fama da matsalolin guda biyu, matsalar babban filin jirgin sama da takogi, wadanda za su ba su damar hulda da ‘yankasuwa daga ko’ina a fadin duniya. Saboda haka ya gode wa Allah bisa wannan dama da suka samu a wannan lokaci.Yanzu haka matafiyan da za su tafi kowace kasa a duniya daga Kaduna ba sai sun je Legas ko Abuja ba, daga Kaduna za su tashi zuwa duk inda suke bukatar zuwa.Sannan sai ya tabbatar da cewa za su bayar da dukkan gudummowar da ta kamata na ganin an ci gaba da gudanar da harkoki a wannan filin jirgi kamar yadda ya kamata.

 

Exit mobile version