A kokarin ci gaba da yaki da lalata da kananan yara, Kungiyar kula da hakkin kananan yara ta Nijeriya, da hadin gwiwar Gidauniyar Jose daga kasar Turai, sun kaddamar da sabon ci gaban da aka samu a wayoyin hannu kirar zamani musamman wanda aka fi sani da ‘Android’ wadda za ta tona asirin masu lalata da kananan yara ta hanyar APP “Stop CSE”
A tattaunawarsa da jaridar LEADERSHIP A Yau a Abuja, shugaban kungiyar ta Jose Foundation, Prince Martin Abhulimhem, ya bayyana cewa, gidauniyarsu ta APP na bakin cikin labaran da take ji yadda ake yin lalata da kananan yara a Nijeriya da ma wasu sassa na duniya baki daya.
Martin, ya ci gaba da cewa tonon asirin da wannan manhaja za ta yi ga masu irin wannan mummunar dabi’a ta lalata da kananan yara, zai sa su shiga taitayinsu, ba kamar a lokutan baya ba da suke cin karensu babu babbaka, saboda kunya da al’adar da ake da ita ta rashin son tonon asirin iyali.
Sannan sai ya bukaci iyaye da yara da su sa manhajar ta APP “StopCSE” a wayoyinsu, domin zai taimaka musu a matsayin hujja wajen neman hakkinsu a kotu.
A karshe, Martin ya ce, kwananan za su shirya taron kara wa juna sani kan yadda za a yi amfani da wannan sabuwar manhaja, da ake fatan ta kawo karshen badala da kananan yara a dukkan duniya