Daga Abubakar Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kaddamar da tsarin ciyar da abinci ga daliban makarantar firamare.
Da yake jawabi a wajen taron gwamna Masari ya yi kira ga matan da za su gudanar da shirin bayar da abincin kyauta ga daliban na firamare da su ji tsoron Allah su kuma tabbatar da samar da abinci mai tsabta da gina jiki ga daliban.
Ya kuma bukaci iyaye mata da su bawa ‘yayayensu damar samun ilmin addini da na zamani da zai taimaka masu a rayuwarsu ta nan gaba tare da kira gare su da su rungumi kasuwanci da sana’o’i da za su taimaka ma su zama a gidajen mazajensu a maimakon dogaro kacokam ga mazajen nasu.
A nata jawabin a wajen kaddamar da shirin, mai ba gwamna shawara a kan ilimin ‘ya’ya mata da cigaban yara Hajiya Binta Abba Dutsinma ta bayyana cewa kimanin daliban makarantun firamare dubu dari tara (900,000) ne zasu amfana da shirin ciyarwar kyauta a makarantu.
Ta kuma bayyana cewa sama da mata dubu goma ne aka dauka domin dafa abincin ga daliban a fadin kananan hukumomi talatin da hudu (34) da jihar ta ke da su.