Kaddara A Wajen dan Nijeriya!  

Abin da nake kokarin bayyana wa shi ne yanayin daya daga cikin dabi’un da suka yi tasiri ga rayuwa da zamantakewar dan Nijeriya bisa ga yadda yake kallon ‘Kaddara’ a ayyukan sa na yau da kullum ta hanyar jingina baki dayansu da Allah, a matsayin ba shi da wani zabi wajen tassarufi da su, a matsayin dama can haka aka rubuta masa su a allon ‘Kudurar’ da yake da ikon gudanar abubuwan da ke kai momo su kawo ga ayyukan bayi.

 

Wannan fagen ilimi ne wanda masana suka yi ta luguden hujjoji a kansa ta hanyar bayar da sakamakon nazari dangane da wanzuwar rabe-raben mazhabobin akida da shari’a a tsakanin al’ummar musulmi, al’amarin da zai kara wa mai karatu hasken cewa dukan duk inda dan Adam yake baya rasa motsi, face sai idan bincike da zurfin ilimi bai kai ma’isar wada ba. Haka zalika, hakan yake taimakon masana a hannun dama da hagu wajen amfani da kowane yanayi domin rike kurwar kwakwalen matsakaitan mutane a matsayin taskar da zata basu damar tafiyar da tunanin duniya irin yadda aka bukata.

 

Idan ana zancen yadda wasu yan Nijeriya ke fassara ayyukan yau da kullum za ka ga yana da alaka da mallamai a ilimin bambance-bambancen muzhabobi ke magana, wanda suka kawo mazhabobin ‘Jabariyya da Kadariyya’ wadanda kowa daga cikin su da yadda yake fassara ma’anar ayyukan mutum tare da jingina su da Allah Madaukakin Sarki. A wajen “Jabriyya” mutum ba shi da katabus wajen gudanar da ayyukansa na yau da kullum face Allah ne yake gudanar dasu da kansa (S.W.T), kuma ba shi da zabi a kan haka- kamar yadda marubucin littafin ‘Milal Wa Nahal, Shaikh Ibni Hazam ya tabbatar. Har wala yau, wannan tsohuwar akida da tunanin Larabawa ce kafin zuwan musulunci, kamar yadda Allah Madaukaki ya bayyana dangane da hakan, a Sura An’am- aya ta 148.

 

A hannu guda kuma, takwarar wannan mazhaba ita ce “Kadariyya” (ba kadiriyya ba), wadda mabiyanta suka tafi a kan cewa dan Adam shi yake da cikakken ikon aiwatar da ayyukansa duk da wani bangaren mabiya mazhabar ya yi hannun riga da hakan. Masana sun bayyana cewa wannan mazhaba ce wadda ta samo asali daga wasu addinai da ke makobtaka da kasashen Larabawan Hizaz, tare da jinginata da wani Banasare mai suna Ma’abad Juny.

 

Idan mun kalli yadda dan Nijeriya ke fassara ayyukan sa na yau da kullum, hakan zai iya alakanta shi da daya daga cikin wadannan mazhabobin, ya sani ko bai sani ba. Kana bisa ga yanayin muhalli irin na nahiyar Afrika, jingina wa Allah nauyin kowane aikin da bawa ya yi, abu ne mai matukar hadari tare da cin karo da hakikanin yadda al’amurra ke gudana a karkashin dokokin Shari’a. dauki misali da kisan kai, rasa wani bangaren dan Adam, duk abubuwa ne wadanda Shari’a ta bayyana matakin da za a dauka ga duk wanda ya aikata su. Amma mafi yawan lokuta, dan Nijeriya zai yi maka aikin ganganci sai ya nuna maka haka Allah ya kaddara. Wanda da abin ayi tambaya ne: me yasa Shari’a ta gindaya hukunci ga irin wadannan ayyuka?

 

Kowace rana hadurra ake yi, kisan ganganci da aikata munanan ayyukan take hakkin dan Adam, na kuskure da na ganganci, amma kusan zancen daya ne: kayi hakuri, haka Allah ya “kaddara”. Kuma har a dokokin kundin tsarin mulkin Nijeriya, kunshe yake da hukunce-hukuncen dangane da irin wadannan kurakuran, amma abin takaici ba a aiwatar dasu. Kuma hakan sakaci wajen bin doka da aiwatar da ita shi ne ya jefa mu mawuyacin halin da muke ciki a yau na tabarbarewar abubuwa.

 

Haka kuma, wannan ne ya bai wa wasu gurbatattun shugabanni cikakkiyar damar ci gaba da sihirce tunaninmu ta hanyar cin karensu babu babbaka wajen tafiyar da mu kan burtalin da suka ga dama, domin ci gaba da jan jarensu iya son ransu ba tare da fuskantar wata turjuya ko kalubale ba, saboda masaniyar da suke da ita kan cewa sun dana mana tarkon da ba zamu subuce ba- sai gyaran Allah. Sun yi imani ba za mu iya motsi ba daga wannan daurin gwarman da suka yi mana- tamau, cikin karkiya.

 

Har wala yau, wannan manufa ce dadaddiya wadda aka kitsata don ci gaba da mallake tunanin dan Adam a hannun yan baranda a kowace kusurwa a duniyar nan, ta hanyar amfani da salo mai ratsa jiki tamkar jini a jijiya wajen dasa shi a kwakwale da zukata. Ya kan dauki dogon lokaci kafin ya zagwanye, ya bi jiyoyi da laka kana ya ratsa kowane bangare, daga nan shikenan an gama.

 

A hannu guda kuma, idan abin ayi tambaya ne: ta wace hanya muka fada wannan kwazazzaben? Da farko abubuwa da daman gaske suna gudana a fadin duniyar nan, ta hanyar tunani, akida, al’ada da yanayin muhallin da mutum yake rayuwa a ciki, kuma suna bambantuwa ne ta la’akari da yadda suke gudana da tasirinsu a rayuwar mutum, wanda ta haka ne za su yi sauki wajen a mallake shi cikin sauki, saboda a ka’idar mutum abu ne mai wahala ka tirsasa shi wajen cimma muradi, dole sai ta irin wadannan hanyoyi masu sauki tare da kama zuciya da kwakwalwar dan Adam.

 

Wanda bisa wannan ne masana a ilimin zamantakewa suka nuna cewa babu abu mafi muhimmanci da tasiri; kuma mai wahalar yaka, kamar akida da al’adu. Sannan ba wai ba a nasara wajen rusasu ko kawo gagarumin sauyin da ake muradi ba- akida da al’ada, ana amfani da yakin kwakwalwa ne wajen rusasu ko sauyasu zuwa matakin da aka ga dama. Saboda kusan kowanen mu shaida ne- ta la’akari da yadda wasu al’adunmu suka yi ko kasa ko sama, kuma da za a tambayi mutum yadda aka yi sai dai ya ce sauyin zamani ne: shi zamanin ai mutum ne yake shiga da fita wajen kyautata shi ko akasin hakan.

 

Ana yakar tunani ne ta ruwan sanyi da taka-tsantsan bisa manufar da masu aiwatar dashi suka tsara tare da ayyana lokaci da muhalli kana da muradin da ake son a cimma, kuma yana tasiri da wanzuwa idan al’umma ba ta fadaka ba, tare da tashi haikan ta nazarci sakamakon da ayyukanta ke jawo mata ba, hatta nagartattun ayyuka ya dace a kalli nasarorin da suka jawo, ballantana akasinsu, wadanda suke mayar da hannun agogo baya a tsarin rayuwar yau da kullum.

Exit mobile version