Daga Rabiu Ali Indabawa
Wasu yan bindiga sun kai farmaki wani gari a Karamar Hukumar Jema’a da ke Jihar Kaduna – Maharan sun kashe mutum bakwai, sun raunata hudu sannan suka kona akalla gidaje hudu. Harin na zuwa ne kimanin kwanaki hudu bayan da ‘yan fashi sun kashe wasu mutane hudu a Kaduna. Jihar Kaduna ta shiga juyayi bayan wani harin sassafe da aka kai sannan aka kashe akalla mutane bakwai a kauyen Ungwar Bido da ke Karamar Hukumar Jema’a.
Channels TB ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba wadanda suka far wa kauyen a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba su ne suka kaddamar da harin. Har yanzu ba a ga wasu yara biyu ba bayan mummunan al’amarin yayin da maharan suka raunata mutum uku da kona gidaje hudu.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa harin ya biyo bayan rahoton kisan wani Isiyaka Saidu.