Rabiu Ali Indabawa" />

Kaduna: Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Luguden Wuta Akan ’Yan Bindiga

Rundunar Sojin Sama

Dakarun sojin sama sun ragargaji ‘yan bindiga a dajin Jihar Kaduna. Sojin sun yi ruwan wuta kan ‘yan fashi a garuruwan da suka hada da Rahama, Tami, Sabon Birni, Galadimawa, Ungwan Farinbatu, Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyelloda sauransu. Sun kuma yi nasarar hallaka ‘yan bindiga da dama da ke kokarin tserewa da dabbobi. An kashe ‘yan bindiga da dama yayin da jiragen sama ke gudanar da aikin leken asiri a wasu wurare a jihar Kaduna.

Jiragen saman rundunar sun ragargaji ‘yan fashi a garuruwan Rahama, Tami, Sabon Birni, Galadimawa, Ungwan Farinbatu, Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello, Dogon Dawa, Ngade Allah, Kidandan, da kuma yankunan da ke kusa da karamar Hukumar Birnin Gwari da Giwa. Samuel Aruwan, Kwamishinan ma’aikatar msaron cikin gida na jihar Kaduna, ya bayyana a ranar Laraba, cewa bayanan aikin da aka gabatarwa Gwamnatin Jihar ya nuna cewa duk da cewar an gudanar da cikakken bincike a kan yankin baki daya, ba a ga wani abu ba.
Tawagar sun ci gaba da gudanar da aiyuka a Sabon Madada, Babban Doka, Gwaska, Gajere, da kuma garuruwan da ke kusa da su. A Sabon Madada, an ga ‘yan fashi tare da shanu da yawa suna gudu daga garin a hanyar zuwa gabashin wurin. Nan take aka fafata da su sannan aka kashe su. Sauran wuraren sun bayyana cikin kwanciyar hankali ba tare da fuskantar wata barazanar ba banguard ta ruwaito. Gwamna Nasir El-Rufai ya godewa matukan jirgin saboda aikin da suka yi ya kuma ya yaba da kokarinsu a yankunan. Za a ci gaba da aikin sintiri ta sama a yankin gaba kaya.

Exit mobile version