Connect with us

WASANNI

Kaf Ingila Babu Kamata — In Ji Mourinho

Published

on

Kociyan kungiyar Manchester United Jose Mourinho ya ce ya fi ragowar masu horar da kungiyoyin gasar firimiya a halin yanzu, “don sau uku yana lashe kofunan gasar a zaman da yayi sau biyu a Chelsea.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a gida a hannun kungiyar Tottenham a ranar Litinin din data gabata.

Da yake magana kan shan kayen da kungiyar tayi a Old Trafford, Mourinho ya ce idan mutane sun san ma’anar kwallaye ukun da aka sawa Manchester United, to za su san cewa shi ya fi sauran masu kula da kungiyoyin gasar Firimiya.

Mourinho ya ce, hakan ya faru ne domin shi ya ci gasar Firimiya sau uku yayin da duka sauran takwarorinsa na gasar firimiya a yanzu sun ci gasar ne sau biyu kacal jumulla.

Sai dai dan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, ya ce nasarar da kungiyarsa ta samu a kan Man U a Old Trafford sun isar da wani babban sako.

A wata hira da ya yi da manema labarai dan wasan da ya ci kwallo daya a lokacin da Tottenham  ta lallasa Manchester United da ci 3-0.

Harry Kane Ya ce: “Mun isar da babban sako ne mu zo nan kuma mu yi nasara kamar yadda muka yi – babban sako ne, Mun so mu fara wannan kakar da kafar dama kuma mun samu nasarori uku cikin wasanni uku saboda haka Mun fara da sa’a.”

Kane ya ce ragowar ‘yan kungiyarsa ta Tottenham ba su yi wasa da kyau ba kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma kwallon da ya ci bayan an dawo daga hutun ta yi matukar taimaka wa kungiyar sosai.

Bayan Kane ya ci kwallon ne dai Lucas Maura ya zura kwallaye biyu a ragar Manchester United sai dai Manchester United tasamu dama kala-kala domin takai hare hare wadanda bata samu nasara ba.

Wannan ya sa Tottenham ta zama ta biyu a teburin gasar Firimiya yayin da take da maki daya da Liberpool, wadda ke saman tebur, sai dai Liberpool ta fi su yawan kwallaye a raga.
Advertisement

labarai