Abubakar Abba" />

Kafa Cibiyoyin Kula Da Lafiya Ne Mafita Wajen Kawar Da Kansa –Dakta Maryam

asibitoci

Shugabar gidauniyar mace ta duba mace wato Women For Women Dakta Maryam Abubakar ta yi kira da tattausar murya ga matakan gwamnati uku da ke kasar nan su kara mayar da hankali wajen yaki da cutar kansa, musamman ta hanyar kakkafa cibiyoyi na musamman da samar da na’urorin yin gwajin cutar.
A hirar ta da wakilin LEADERSHIP A YAU a Kaduna, Dakta Maryam ta ce, koda take matakan gwamnatin uku suna iya na su kokarin, musamman ta hanyar wayarwa da alumna kai, amma akwai bukatar, matakan uku su kakkafa cibiyoyi na musamman don cin karfin cutar a matakan ta na farko. Sai dai, Dakata Maryam ta nuna takaicinta a kan yadda wasu yan kasar nan ba sa zuwa asibiti ana duba su domin a gano lamomin cutar.
A cewar ta, “Cutar tana farawa ce ta hanyar futowar dan tsiro har dan tsiron ya girma ya zama kansa ta dinga cin jikin bil’adama, mutane sun fi saninin kansar nono, kansa ba inda ba ta shiga a jikin bil’adama, ba mata kadai suke yin ta ba har ma maza.”
Ta ci gaba da cewa, “Akwai kansa ta gaban mace, akwai ta nono, ta mahaifa, koda, ta baki duk maza da mata suna iya kamuwa, akwai ta maraina da mata ke yi.”
Shugabar wacce kuma ita babbar jami’a ce a asibiti Fateema Clinic ta kara da cewa, “Rashin daukar mataki tun da wuri ga wanda ya kamu, yin hakan a wani lokacin ko an yi aikin, ba zai yi wani tasiriba.”
Dakta Maryam ta sanar da cewa, idan ta kama mutum baya jin wani zafi, tana fara yin zafi ne in ta ci jikin mutum, ga mata su dinga zuwa asibiti ana duba bakin mahaifarsu, tun tana ‘yar kadan ana yin gwaji za a gano ta da wuri don magance ta.
Ta yi nuni da cewar, “Tana shafe shekaru a jikin mutum, amma bai san ya kamu da ita ba, mutum bai sani sai in ta fara cin karfin jikinsa, tana shafar har cikin zuciyar bil’adama, akwai ta cikin jini ana kuma gadon ta, wani ma daga kakansa ya ke gadon ta, amma babbar mafuta shi ne, mutane su dinga zuwa asibiti ana duba lafiyarsu akai-akai da kuma yi masu gwaje-gwaje.
Da take tsokaci a kan kwayoyin cutar Dakta Maryam ta ce, “Maza da mata duk suna iya kamuwa da kwayoyin cuta, amma mafita ita ce, a tabbatar da tsaftar muhalli, wanke ban-daki ta hanyar yin amfani da magungunan kashe kwayin cutar, shan magani a kan lokaci ga wanda ya kamu da kuma zuwa asibiti don yin gwaje-gwaje.

Exit mobile version