Kafa Hukumar Kula Da Nakassasun Nijeriya Da Dawo Da Martabarsu

A ranar Litinin, 24 ga Agusta na 2020 ne, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince tare da nada shugabannin hukumar kula da nakasassu ta kasa, wato ‘National Commission for Persons with Disabilities’, kamar yadda Dokar Hana Wariya Ga Nakasassu ta 2019 ta tanadar.

Mai magana da yawun Shugaban kasar, Mista Femi Adesina, ne ya fara yi wa ’yan kasar wannan albishir a cikin wata sanarwa da ya bayar ranar Litinin din karshen watan, inda ya ce, Hukumar za ta kasance ne a karkashin Ma’aikatar Harkokin Agaji tare da Jinkai ta Tarayya, wacce Hajiya Sadiya Umar Farouk ta ke a matsayin minista.

Dokar dai ta tanadi cewa, za a samar da shugaba tare da membobi shida wadanda dukkan su nakasassu ne daga sassan kasar nan guda shida wadanda za su jagoranci Majalisar Gudanarwar hukumar na tsawon shekara hudu, kuma za a iya kara masu wa’adin shekara hudu na karshe, tare da amincewar Majalisar Dattawa.

Haka kuma dokar ta ce za a nada Babban Sakatare, wanda ke karkashin Majalisar Gudarwar, don aiwatar da ayyuka da tsare-tsaren hukumar, wanda kuma shi ma tilas ya kasance nakasasshe ne, kuma zai yi wa’adin shekara biyar, sannan za a iya dada masa wa’adin shekara biyar na karshe.

Wannan ba karamin cigaba ba ne, idan a ka yi la’akari da yadda a ka dauki masu buakata ta musamman a kasar, inda a lokutan baya a ke nuna mu su kyama a zahirance kuma a bayyane, domin hatta gwamnatoci su na nuna mu su kyama. Hakan yak an fito fili ne musamman a lokutan da za a gudanar wani shiri, kamar na wasanni, a Nijeriya, wanda ya shafi kasashen duniya, inda gwamnati ta kan rika kame nakasassu da mabarata a kan hanyoyi ta na saye su, don gudun kada bakin da za su shigo Nijeriya su rika ganin su. Wannan kyama ce a zahirance, kuma hakan ya saba da manufofin Majalisar dinkin Duniya na kare hakkin bil adama da kuma marasa galihu.

Saka hannu da Shugaba Buhari ya yi kan dokar a bara da kuma nada hukumar a bana ya na uni da cewa, Nijeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen kare hakkin marasa galihu da nesanta kai daga nuna kyama ga wadanda Allah ya sanya wa wata lalura. Kafa hukumar gudanarwar da gwamnatin NIjeriya ta yi ya na nuni da cewa, shugabanta mai bukata ta musamman ne da wasu daga cikin mambobinta, inda hakan ya nufin nuna kyama ta hanyar boye nakasassu a kasar ya zama tarihi kenan ko a iya haka a ka tsaya, ballantana kuma za su samu kulawa ta musamman fiye da baya, domin sun zama masu uwa a bakin murhu kenan daga yanzu.

Tilas a yaba wa wannan gwamnati bisa wannan kokari da ta yi wa mutanen da wasu ke kallo a matsayin su ne karshen marasa galihu a kasar, wato nakasassu ko masu bukata ta musamman, a karkashin jagorancin MInistar Jinkai da Agaji, Hajiya Sadiya Umar Farouk, wacce ta jajirce, don ganin ta janyo hankalin Shugaba Buhari wajen daga kafa, don fara aiwatar da dokar, wacce tun a bara a ka sanya wa hannu.

A nan za mu iya yarda da ikirarin ministar na cika alkawarin da ta dauka a lokacin da a ka nada ta a matsayin Ministar Jinkai ta farko a tarihin kasar, wacce ta ci alwashin ganin nakasassu sun samun cin gashin kansu.

A cikin wata sanarwa, Minister ta ce, ‘’Wannan ranar farin ciki ce a gare ni wadda buri na ya cika, ganin cewa wani sashe na mutane masu matukar bukatar tallafi wadanda na ke jin tausayin su, a karshe sun samu hukuma tasu ta kan su, har an nada mata shugabanni wadanda za su tafiyar da al’amurran ta, kuma ta kare hakkokin su, sannan ta sama masu kyakkyawan yanayi da za su inganta rayuwar su har su bada tasu gudunmawar ga cigaban al’umma baki daya.”

Ministar ta mika godiyar ta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda rattaba hannu da ya yi kan Dokar Hana Nuna Wariya Ga Nakasassu ta Shekarar 2019 a bara, wadda ta bada damar a kafa hukumar.

Farouk ta ce: ‘’Ta hanyar amincewa da nadin shugaba da Babban Sakatare da sauran membobin cibiyar gudanarwar hukumar, Mai Girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara nuna sadaukarwar sa ga batun inganta rayuwar mutane marasa galihu a Nijeriya, kuma ya ba su damar su ma su ci moriyar dukkan hakkokin su a matsayin su na ‘yan Nijeriya.”

Daga nan sai ta taya murna ga nakasassun da ke Nijeriya wadanda ta ce yawansu ya kai mutum miliyan 30. Saboda haka wannan babbar nasara da a ka samu, kuma ta yi kira a gare su da su yi amfani da wannan dama da a ka sama mu su yadda yakamata.

Hajiya Sadiya ta ce: ‘’Ina taya murna ga ‘yan’uwa na maza da mata wadanda ke rayuwa da wata nakasa a Nijeriya saboda wannan cikar buri, kuma ina kira a gare ku da ku yi amfani da damar samun wannan hukuma wajen hada kan ku don gina rayuwa mai albarka.”

Har ila yau, ministar ta taya murna ga shugabannin hukumar da aka nada, Dr. Hussaini Suleiman Kangiwa, tare da yin kira a gare su da su yi aiki tukuru.

Ta ce, “Ina taya ku murna sosai, kuma ina kira a gare ku da ku dauki wannan wannan nadi naku a matsayin wata dama da ku ka samu ta zama shugabanni na farko na hukumar, don haka ku shimfida fandeshi mai karko na hukumar, tare da tunanin cewa samun ingancin rayuwar mutum sama da miliyan 30 da ke fama da nakasa a Nijeriya yanzu ya danganta kan yadda ku ka aiwatar da aikinku.”

Yanzu dai dabara ta ragewa mai shiga rijiya ga wadannan shugabanni, domin an ba su wuka da nama, sai yanka kawai. Za a iya cewa, Fadar Shugaban kasa da Ma’aikatar Jinkai sun yi nasu!

Exit mobile version