Daga Muhammadu Awwal Umar, Minna
Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da kwamitin hadin gwiwa kan tattara kudaden shiga domin yin biyayya da dokar hakar ma’adanai a karamar hukumar Kankara.
Kwamishinan bunkasa albarkatun kasa Alhaji Mahmud Kanti Bello wanda wani Darakta daga ma’aikatar ya wakilta ya kaddamar da kwamitin.
Ya ce yunkurin na daga kokarin gwamnatin gwamna Aminu Bello Masari na bullo da hanya daya domin tattara kudaden shiga a bangaren hakar ma’adinai.
Kwamishinan ya kara da cewar, kwamitin zai kuma tabbatar da ganin ana gaggauta biyan kudaden shigar tare da tabbatar da ganin komai na tafiya kan ka’ida a bangaren kokarin da ake yi na samarwa bangaren lasisin ci gaba da aiki.