Daga CRI Hausa
A ranar 14 ga wata, an wallafa wani rahoto a shafin yanar gizo na jaridar “Friday Weekly” ta Jamus, mai taken “Buri mafi girma a duniya”, inda aka gabatar da sakamakon da kasar Sin ta samu a fannoni daban daban, ciki har da nasarar shawo kan annobar COVID-19, da sake bunkasar cinikayyar waje, da rage fitar da gurbatacciyar iska, da yaki da talauci da sauransu.
Rahoton ya nuna cewa, an kira taruka biyu na kasar Sin a birnin Beijing bisa shirin da aka tsara, wato ba a jinkirta tarukan kamar yadda aka yi a bara ba, lamarin da ya alamta cewa, kasar Sin ta riga ta yi cikakkiyar nasara, wajen shawo kan yaduwar cutar COVID-19, kuma duk da cewa, ba a yi wa daukacin al’ummun kasar allurar rigakafin cutar ba, amma alluran da kasar take samarwa, suna biyan bukatun kasar matuka, a don haka tana samar wa sauran kasashe masu tasowa tallafin alluran, haka kuma tana samar wa wasu kasashen Turai tallafin.
Kana Sinawa suna mai hankali kan shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 14. Kuma abu mai faranta rai shi ne, duk da cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya taba samun koma baya a farkon shekarar 2020, amma tun daga rubu’in biyu na bara, tattalin arzikin kasar ya farfado cikin sauri.
A cikin rahoton, an yi nuni da cewa, yanzu haka cinikayyar waje ta kasar Sin ta sake samun wadata, har ta rinjayi Amurka a Turai, kana Jamus ma tana bukatar kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa, idan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana, zai kai kaso 6 bisa dari, kuma ko shakka ba bu, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa wajen cinikayyar dake tsakanin kasa da kasa.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, an ga alamar cewa, kasar Sin ta yi cikakkiyar nasarar yaki da talauci a fadin kasar, kuma sabuwar dokar dake shafar rayuwar al’ummun kasar ta fara aiki a farkon shekarar bana. Hakan babban sakamako ne da kasar Sin ta samu, a yayin da Sinawa suke taya murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS. (Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)