Kafar Watsa Labarai Ta Khazakstan: Sirrin Kasar Sin Na Samun Ci Gaba Cikin Sauri

Daga  CRI Hausa

A ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, jaridar DK News ta kasar Khazakstan, ta wallafa wani bayani mai taken “Mane ne sirrin kasar Sin na samun ci gaba cikin sauri?”, inda aka bayyana cewa, bisa jagorancin jam’iyya mai mulki wato jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), jama’ar kasar sun samu raya kasarsu sosai, tare da samar da damammakin kyautata tattalin arziki ga kasashe daban daban.

Marubucin bayanin ya ce, wasu abubuwa guda 6 sun baiwa kasar Sin damar samun ci gaba cikin matukar sauri. Wadannan abubuwa a cewar jaridar su ne:
Da farko, JKS ta yi nasarar hada tunanin Marxism da hakikanin yanayin da kasar Sin take ciki, don tsara wasu manufofi masu dacewa, inda har take dinga daidaita manufofi, tare da gwajin wasu sabbin dabaru, da nufin raya kasa.
Na biyu, JKS ta tsaya kan manufar daukaka dimokuradiya gami da da’a, lamarin da ya sanya ake iya cimma daidaito da daukar matakai cikin sauri a cikin JKS.

Na uku shi ne, yadda ake dora matukar muhimmanci kan samun ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.

Na hudu shi ne, yadda ake mai da moriyar jama’a gaba da komai. Inda JKS take kokarin wakiltar babbar moriyar daukacin al’ummun kasar.

Sa’an nan na biyar, yadda JKS take kokarin yaki da cin hanci da rashawa.
Kana na shida, yadda JKS take tsayawa kan ra’ayin raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Abin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya, da neman samun ci gaba tare da sauran kasashe, da taimakawa sauran kasashe wajen dakile annobar cutar COVID-19, dai dai sauransu. (Bello Wang)

Exit mobile version