Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Kafar Watsa Labaran Kenya: Sin Na Daukar Hakikanin Matakan Raba Allurar Rigakafin COVID-19 Bisa Adalci

by Sulaiman Ibrahim
February 21, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Kafar Watsa Labaran Kenya: Sin Na Daukar Hakikanin Matakan Raba Allurar Rigakafin COVID-19 Bisa Adalci
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga CRI Hausa

A ranar 19 ga wata, agogon kasar Kenya, jaridar The People ta kasar ta wallafa wani rahoto, inda aka yaba wa kasar Sin bisa cika alkawarin da ta yi, tana daukar hakikanin matakai domin rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19 bisa adalci a fadin duniya.
A cikin rahoton, an yi nuni da cewa, annobar COVID-19 ta haifar da rikici a fadin duniya, yanzu haka yawon shakatawa tsakanin kasa da kasa ya katse, tattalin arzikin duniya ya koma baya, siyasar nuna fin karfi da tunanin yakin cacar baka sun sake kunnowa, kuma ra’ayin bangaranci da ba da kariya su ma suna sake bazuwa, ana iya cewa, bil Adama suna fuskantar hadari da kalubaloli da ba su taba ganin irinsu ba a baya, kana wasu kasashe suna siyasantar da annobar, suna adawa da dabarun kimiyya, har suna tattara allurar rigakafin cutar ta hanyar yin amfani da karfin siyasa, tare kuma da yin watsi da bukatun kasashen da suke fama da koma bayan tattalin arziki, alkaluman MDD ya nuna cewa, kasashen duniya 10 sun mallaki alluran rigakafin cutar COVID-19 kaso 75 bisa 100 na yawan alluran rigakafin a fadin duniya.
Rahoton ya jaddada cewa, ya dace sassa daban daban su hada kai domin yaki da nuna fifiko kan al’ummun kasashe daban daban, yayin da ake raba allurar rigakafin annobar, ta yadda za a raba allurar bisa adalci, musamman ma a kasashen dake fama da rikici.
A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta riga ta samar da tallafin allurar rigakafin ga kasashe masu tasowa da yawansu ya kai 53, kuma ta fitar da allurar ga kasashe 22, kana ta samar da allurar biliyan 1 ga shirin COVAX domin biyan bukatun kasashe masu tasowa.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

SendShareTweetShare
Previous Post

Taimakon Da Sin Ke Baiwa Ajandar Kare Muhalli Zai Gaggauta Farfadowa Daga COVID-19

Next Post

Cibiyar Kirkire-kirkire Ta Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Za Ta Samar Da Himma Ga Kasashen Afirka Wajen Raya Kansu

RelatedPosts

Muradun Raya Kasar Sin Sun Baiwa Duniya Tabbacin Bunkasuwa

Muradun Raya Kasar Sin Sun Baiwa Duniya Tabbacin Bunkasuwa

by Sulaiman Ibrahim
29 mins ago
0

Daga CRI Hausa A yau Juma’a ne aka bude taron...

An Gudanar Da Taruka Biyu Na Bana A Wani Muhimmin Lokaci

An Gudanar Da Taruka Biyu Na Bana A Wani Muhimmin Lokaci

by Sulaiman Ibrahim
34 mins ago
0

Daga CRI Hausa A wannan shekara ce, Jam’iyyar Kwaminis ta...

Li Keqiang: Karuwar GDPn Sin Zai Iya Zarce Kashi 6% a 2021

Li Keqiang: Karuwar GDPn Sin Zai Iya Zarce Kashi 6% a 2021

by Sulaiman Ibrahim
37 mins ago
0

Daga CRI Hausa Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar...

Next Post
Cibiyar Kirkire-kirkire Ta Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Za Ta Samar Da Himma Ga Kasashen Afirka Wajen Raya Kansu

Cibiyar Kirkire-kirkire Ta Hadin Gwiwar Sin Da Afrika Za Ta Samar Da Himma Ga Kasashen Afirka Wajen Raya Kansu

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version