Connect with us

HANTSI

Kafin Ka Zabi Macen Da Za Ka Aura, Ka Lura Da Wannan…

Published

on

Farkon abin da namiji zai kula da shi wajen zabar matar aure shi ne, samun fahimta tsakanin ka da wacce ake tunanin zama matarka, yana da kyau ku bi tsari daya da kuma fahimtar iri daya ta yadda za ku tafiyar da rayuwar aurenku kafin ‘ya’ya su zo muku. Ya zamana kun shirya gida wanda ‘ya’yanku za su sami kwanciyar hankali da nutsuwa a cikinsa, saboda koda mai addini ka dauko idan babu fahimtar juna a tsakanin ku, to za ku fuskanci matsaloli da dama.
Rashin samun fahimtar juna yana jawo muku rashin kwanciyar hankalinku, saboda kullum kuna cikin rigima da cin mutuncin juna. A irin wannan lamari wacce irin tarbiyya ce za ku bai wa ‘ya’yan ku.
Idan tun kafin aure ya zamana kuna yawan samun banbancin ra’ayi da yawan sabani da budurwarka, kuma ba ta son irin ra’ayinka, ba ta bin maganarka, ba ta daukan shawararka, to a gaskiya shawarar da zan ba ka kada ku yi aure, saboda samun bambamcin ra’ayi sosai yana kawo rashin zaman lafiya a cikin rayuwar aure. Kenan dole ne ka auri wacce fahimtarka da tsarinka ya zo dai-dai da ita. Ya zamana inda kuka yi sabani bai wuce kashi 20 ba cikin dari, shima kashi 20 din ya kasance ba a manyan abubuwa ba, kamar yawan haihuwa ya zamana kai kana son haihuwa da yawa ita kuma ba ta so dama sauran su.
Mafiya yawan matasa za ku ga suna samun matsala a lokacin suna soyayya, amma sai su ce ai muna yin aure komai zai wuce ai dole ta bi ra’ayina tun da a karkashina take, tun da ni ne da ita a yanzu, ko kuma mace ta yi ta masa halin rashin kyautawa iri- iri, amma sai ya ce idan ta aure ni za ta dai na, ko kuma idan ta shigo gidana dole na yi mata koma meye don ta bi ni. Wadannan shi ne zai sa ku ga ana ta rigima da bala’i a cikin gidan aure, idan har tun a waje mace ba ta mutunta ka, ba ta daraja ka, ba ta da ra’ayi irin ka, rigima kawai za ku yi ta yi da ita idan kun yi aure, duk yanda za ku so ku samar da zaman lafiya to fa ba zai yiwu ba, saboda kun baro shiri tun rani. Mafiya yawan auren yanzu in ka ji matsalolin maza da mata za ka ji rabin su duk saboda bambamcin ra’ayi ne. A nan ina bawa maza shawara kan su duba irin matan da za su aure saboda kaucewa matsalolin da ma’aurata suke samu a yanzu. Bayan guje wa matsaloli, sannan ‘ya’yanka za su sami cikakkiyar tarbiyya domin ka ba su gudummuwar da ta dace lokacin zaban musu mahaifiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: