Yusuf Abdul Yakasai" />

Kafin Mutum Ya Aibata Buhari Ya Kamata Ya Binciki Kansa Tukuna — Sani Sakatare

An bayyana cewa Yan Nijeriya ba mu da kasar da tafi kasarmu ta gado, Nijeriya, don haka kowa ya rungumi abubuwan da za su kawo kasar alherai da yawa.
Alhaji Sani Sakatare Abubaka Legas, ya yi kiran saidan da yake zantawa da wakilinmu a Legas.
Alhaji Sani Sakatare Abubakar wanda yake daya daga cikin shugabannin masu harkar manyan motoci (trailer) a Nijeriya, ya roki Yan Nijeriya su kawar da zalunci a zukatansu sannan su cigaba da nemo hanyoyin da za a kyautata rayuwa yan kasa a tsakanin junansu.
“Mafiya yawanmu Yan Nijeriya bukatunsu suka fi tarewa (self interest) ba na jamaar kasa ba, bukatunsu su tura yanyansu Turai ba ruwansu da yayan talakawa kullum za ka ji suna Buhari ya yi kaza da kaza kowa ya san Buhari ba Babawo bane kuma ba ya cin kayan jamaa. Yanzu a masu cewa Buhari ya yi kaza da kaza da za a ba wani rikon wani waje za ka ga shi ne babban azzalimi. Saboda haka ya ba za mu fuskanci matsala ba sai mun kauce wa son zuciya, mun fuskanci Allah kuma mun so juna da gaskiya sannan tallafi zai zo daga Allah. Da zarar alumma sun karkata da son zuciya mutun ko kansa ne yake ciwo saika ji ya ce Buhari ba adalci ba tsoron Allah.
“Masu cewa mu talakawa muke karewa, da za ka tambaye shi me yake wa talakawa a jiharsu ko a garinsu ko kuma ya wari wani abu da za a ringa yi wa talakawa aiki da shi, sai dai yawan sukan Buhari babu wani abu da shi ya fara gwadawa kafin ya fara sukan Buharin, saboda haka ba kishin kasa ba biyan bukatarsu kawai suke karewa. Ka ga ba za ka yi wanka da kashi ka ce za ka yi kyalli ba ko kamshin turare ba” ya bayyana.
Alhaji Sani Sakatare yak um yi kira ga Yan Arewa mazauna Legas su himmatu wajen mayar da hankali a kan abin da ya kai su can, tare da kiyaye kima da martabarsu da kuma laakari da inda suka fito.

Exit mobile version