Balarabe Abdullahi" />

Kafofin Sadarwa Na Zamani Na Bukatar Sa Idon Hukuma –Kabiru Kafinta

An bukaci gwamnatin tarayya musamman hukumar sadarwa ta kasa da ta tashi tsaye na ganin ta kawo karshen yadda wasu mutane suka dauki kafafen sadarwa na zamani hanyoyi ne da za su ci mutuncin shugabannin addini da sauran manyan mutane da suke da kima a idon al’umma.

Wani fitaccen mai tsokaci kan al’amurran yau da kullun da ke Sabon garin Zariya a jihar Kaduna mai suna Alhaji Kabiru Kafinta ya bayar da shawarar a lokacin  day a zanta da wakilinmu da ke Zariya, a kan wannan matsala da a yau ta zama ruwan dare a kafafen watsa labarai na zamani.

Alhaji Kabiru Kafinta ya bayar da misali da yadda babu kunya babu tsoron Allah wasu  wadanda ba su san darajar shugabannin addini ba, kawai domin wadannan shugabannin ba fahimta daya suke da wannan malami ba, sai ka ga an sa hotonsa, tare da yin rubutun kazafi ga wannan malami da kowa ya san ya sami karbuwa a sassan duniya ba Nijeriya kawai ba.

Baya ga shugabannin addini da ake yi ma su batanci, a cewar Alhaji Kabiru sauran shugabannin al’umma ba a barsu ba, wannan matsala, kamar yadda y ace, in har gwamnatin tarayya musamman hukumar sadarwa ta kasa a karkashin minister Fantami bat a gaggauta kawo karshen wannan matsala ba, za ta iya zama wata matsala ta daban, da a nan gaba, murkushe matsalar daga gwamnati zai iya zama gagara badau.

Da kuma Alhaji Kabiru Kafinta ya juya ga al’ummomin da suke yin wadannan batanci  a kafafen watsa labarai na zamani, ya ce, ya zama wajibi a garesu su rika tuna yadda addinin da suke bi ya yi umurni da a rika girmama manya, musamman shugabannin addini , a cewarsa, babu uzuri ga mai batanci ga wani malami das hi a tunaninsa, ba fahimta daya suke da shi ba.

A dai zantawar da wakilinmu ya yi da Alhaji Kabiru ya kuma yi kira ga shugabannin kungiyoyin addini a duk inda suke a Nijeriya, da su zauna teburi guda, su kuma tattauna na yadda za a kawo karshen wannan matsala da ta ke zama silar kara rarrabuwan kan al’ummar musulmi, da kuma nuna wa duniya yadda al’ummar Nijeriya suke daukar shugabannin addinin da a sassan duniya, ma su daraja ne , amma, a cewarsa, sai aka sami akasin haka a Nijeriya a yau.

A karshe, Alhaji Kabiru Kafinta ya yi kira ga ‘yan majalisar tarayya da kuma na wakilai, das u ba ministan sadarwa Shekh Fantami duk goyon bayan da suka dace, a duk lokacin day a gabatar da wasu kudurorin kawo gyara a matsalolin sadarwa ke ciki a Nijeriya, ya ce, duk gyaran da aka yi, su ma za ta yi amfani a garesu, ba shugabannin addinin kawai ba zai yi amfani ba.

Exit mobile version