CRI Hausa" />

Kafofin Watsa Labaran Birtaniya: Huawei Zai Kai Bankin HSBC Kara Domin Samun Muhimman Takardun Bankin

Rahotannin da kamfanin BBC da jaridar The Guardian na kasar Birtaniya suka bayar sun nuna cewa, a ranar 12 ga wata, agogon kasar, lauyan babbar jami’ar kudi ta kamfanin Huawei na kasar Sin Meng Wanzhou zai gabatar da kara ga babbar kotun birnin London domin samun muhimman takardun bankin HSBC.

Kamfanin Huawei ya dauki matakin ne domin shaida cewa, karar da kasar Amurka ta kai madam Meng Wanzhou kan boyewa bankin HSBC huldar dake tsakanin kamfanin Huawei da kamfanin fasaha na Skycom na yankin Hong Kong na kasar Sin, inda sanadiyyar hakan, bankin na Birtaniya ya ci gaba da hidimtawa Huawei, ba ta gaskiya ba ce.
Jaridar The Guardian ta ruwaito kalaman kamfanin Huawei cewa, kamfanin ya bukaci kotun London da ta ba da umurnin samar da bayanan da abin ya shafa, alal misali ma’aikatan bankin HSBC nawa ne suka san taron da aka kira a Hong Kong, da abubuwan da aka tattauna yayin taron, da adadin ma’aikatan bankin da suka san sakamakon taron, da sauransu.
A watan Yulin bara rahotannin manhajar watsa labarai ta jaridar The People’s Daily ta kasar Sin sun bayyana cewa, Amurka ta gabatar da “takardun karar da aka yi rajista” ga kotun kasar Canada, inda ta bayyana cewa, babbar jami’ar kudin kamfanin Huawei Meng Wanzhou ta boyewa bankin HSBC huldar dake tsakanin kamfaninta da kamfanin fasaha na Skycom na yankin Hong Kong na kasar Sin, inda bankin HSBC na Birtaniya ya ci gaba da samar da hidima ga Huawei, a sanadiyyar haka, bankin HSBC ya sabawa dokar takunkumin da Amurka ta sanyawa Iran, har ya gamu da matsalar aikata laifi, a don haka an yanke shawara cewa, Meng Wanzhou ta yaudari bankin HSBC.
Amma hakika kamfanin HSBC ya yi karya, ya san huldar dake tsakanin kamfanin Huawei da kamfanin Skycom na yankin Hong Kong, saboda an gano cewa, kamfanin Skycom na Hong Kong da kamfanin Huawei suna gudanar da hadin gwiwa a yankunan kasar Iran, shaidun mai kwari sun nuna cewa, bankin HSBC ya san harkokin kamfanin Huawei a Iran, kuma a shekarar 2010, sakwannin da aka tura tsakanin bangarori uku wato bankin HSBC da kamfanin Huawei da kuma kamfanin Skycom sun shaida cewa, bankin HSBC ya san huldar dake tsakanin Huawei da Skycom sosai, kana daga takardun harkokin kudin kamfanin Skycom tsakanin shekarar 2009 zuwa 2010 da kamfanin Huawei ya tura ga bankin HSBC, an lura cewa, bankin HSBC ya fahimci daukacin harkokin kamfanin Skycom na Hong Kong dake Iran.
Hakazalika, jaridar The Guardian ta ruwaito kalaman lauyan madam Meng Wanzhou cewa, an jirkita takardun manhajar PPT da ta gabatar wa bankin HSBC, domin ana son yada jita-jitar wai Meng Wanzhou ta boye huldar dake tsakanin kamfanin Huawei da kamfanin Skycom na Hong Kong.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version