CRI Hausa" />

Kafofin Yada Labarai Na Amurka: Kasuwannin Sin Na Janyo Hankulan Masu Zuba Jari Na Kasa Da Kasa

Tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa yadda ya kamata a 2020,a gabar da aka yi fama da matsalar yaduwar cutar COVID-19, jimlar tattalin arzikin kasar ta kafa wani sabon matsayi zuwa yuan trillion dari 1, karfin tattalin arziki da yanayin bunkasuwarsa cikin gida a nan gaba, sun janyo hankulan kafofin watsa labarai na kasar Amurka.

Tashar yanar gizo ta jaridar Wall Street ta kasar Amurka ta fidda bayani cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da 2.3% cikin shekarar 2020, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ita ce kasa daya kacal cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki wadda ta samu karuwar tattalin arziki a gabar da ake fama da matsalar yaduwar annoba.
Haka kuma kafar yada labarai ta CNBC ta kasar Amurka ta bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2020, ta janyo hankulan masu zuba jari na kasashen duniya, bisa hasashen da kamfanin Macquarie ya yi, a kasuwannin sha’anin kudi, takardun lamunin kasar Sin da masu zuba jarin kasashen ketare suka saya ya ninka sama da sau biyu a shekarar 2020. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version