Kaftin Din Super Eagles, Ahmed Musa Ya Bukaci A Gaggauta Kawo Karshen Kashe-kashen Rayuka A Benuwe
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kaftin Din Super Eagles, Ahmed Musa Ya Bukaci A Gaggauta Kawo Karshen Kashe-kashen Rayuka A Benuwe

bySulaiman
4 months ago
Ahmed Musa

Kaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Ahmed Musa, ya yi kira ga shugabannin siyasar kasar da su gaggauta dakile tashe-tashen hankula a jihar Benuwe. Musa, wanda ya yi Allah wadai da kashe-kashen da ake yi a jihar kwanan nan, ya kuma bukaci shugabannin da su dauki kwakkwaran mataki don hana ci gaba da zubar da jini a jihar.

A cikin wata sanarwa da ya dora a shafinsa na X, kaftin din na Super Eagles ya bayyana matukar damuwarsa game da karuwar tashe tashen hankula, yana mai bayyana hare-haren a matsayin “wani abu mai kona zuciya” Musa ya rubuta “Mutane nawa ne za a rasa kafin a dauki mataki na gaske, ba za mu iya ci gaba da yin Allah wadai da tashin hankali sannan mu ci gaba ba, kada mu jira har sai abin ya faru kusa da gida ko kuma ga wani da kuka sani kafin ku dauki matakin da ya dace”.

  • 2025 UTME: Cibiyoyin Zana Jarabawar 11 Na Fuskantar Barazanar Dakatarwa – JAMB
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 4 Da Manoma A Katsina

Dan wasan na kungiyar Kano Pillars ya jaddada bukatar daukar matakan da suka dace daga shugabanni, inda ya bayyana cewa, “Mulki ba kawai lokacin zabe ba ne, muna bukatar aiyuka akai-akai, Benuwe ta cancanci zaman lafiya, Nijeriya ta cancanci zaman lafiya”, in ji shi.

Daga karshe Musa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 200 ne aka kashe a wani hari da aka kai a Yelwata da ke karamar hukumar Guma, wanda galibi ya hada da ‘yan gudun hijirar da ke neman mafaka a wani cocin Katolika na yankin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Next Post
An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana

An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version