Kai Hare-Hare: Ku Dinga Daukar ‘Yan Sanda Tamkar Bil Adama -Nwabianke

'Yan Sanda

Daga  KALU EZIYI,

Jami’in kwamitin taimaka wa ‘yan sanda  (PACC) Anthony Nwabianke ya yi kira da a dinga fahimnatr juna da kuma yin kira ga ‘yan Nijeriya da su  daukar ‘yan sanda tamkar bil adama, musaman domin su sauke nauyin da aka dora masu.

Anthony Nwabianke ya bayyana haka ne a yayin da ya tattauna da manema labarai jim kadan bayan kammala taron gudanar da addu’a a kwana daya ga ‘ayan sanda da ke a yankin Kudu Maso Yamma a garin  Umuahia da ke a cikin jihar  Abia.

Ya yi nuni da cewa, idan akayi la’akari da yawan hare-haren da wasu ‘yan bingiga suka  kai wa ‘yan sanda da kuma kone  wasu caji ofis dinsu a wasu sassan kasar nan ba tare da wata hujja ba, hakan abu ne da bai dace ba.

A cewar Anthony Nwabianke, su ma ‘yan sandan suna da iyalai, kuma su na da nasu mafarkan da suke son cimma buri kamar kowa, inda kuma ya kira ga irin wadannan ‘yan bindigar masu kai hari da su daina su kuma gabatar da korafin su ga hukumar da ta dace

Nwabianke ya yi nuni da cewa- kai hare-haren a caji ofis na ‘yan sandan na da matukar illa, inda ya yi nuni da cewa hakan zai bai wa sauran masu aikata manyan laifukka wajen kustawa cikin alummmo domin aikata ta’asa da kuma kara dakuse karsashin jam’’an tsaro kan gudanar da aikinsu.

Jami’ian kwamitin ya kuma ankarrar da masu kai hare-haren cewa, akasarin kayan da suke lalata wa, kodai gwmanatin ce ta gina su ko kuma alumma, inda ya yi nuni da cewa, akwai kuma guraren da ake taimaka wa jami’an na ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukansu.

Anthony Nwabianke ya kuma yi kira ga matakan gwamnati uku na kasar nan, das u dinga magance dukkan matsalolin da suka kunno kai da kuma ayyukan masu fafutuka, musamman domin a magance dukkan wata barazanar da zata shafi zaman lafiya

A karshe, Nwabianke ya yi amfani da damara wajen jinjina wa Sifoto Janar na ‘yan sanda na kasa Usman Baba kan kaddamar da shirin dawo da zaman lafiya a yankin Kuidu Maso Yamma (OPRP), inda ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a wanzar da shirin bisa  bin doka da oda.

Exit mobile version