Rabiu Ali Indabawa" />

An Kai Hari A Birnin Ouagadougou Na Burkina Faso

Kasar Ghana ta soma fuskantar barazanar ‘yan fashi da makami musamman a harabar bankuna da kamfanonin canji da sauran wuraren da ake hada-hada da kudi

An bayyana cewa kasar Ghana na fuskantar barazanar ‘yan fashi da makami musammam a birnin Accra da Tema inda har sakamakon irin wannan lamari ya yi dalilin mutuwar wani dan taliki, Mustapha Hamid.

To sai dai duk da cewa jami’an tsaro na iya bakin kokarin su amma har yanzu da sauran rina a kaba, domin ko kawo yanzu ba mutun daya da aka samu nasarar kamawa kan aikata wannan danyen aiki.

Fashi da makamin da ya addabi biranen biyu ya fi aukuwa ne a harabar bankuna da wuraren da ake canji kudaden waje ko aika da kudi waje

 

Exit mobile version