An Kai Hari Makarantar Mata A Yobe

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari wata makarantar mata na kwana da ke garin Dapchi a jihar Yobe.

Rahotan ya bayyana cewa,  maharan sun afkawa garin ne a cikin motocin akori kura yayin da  su ka isa makarantar inda suka yi ta harbe-harbe kuma tare da tayar da abun fashewa a garin.

Rahoton ya kara da cewa, daliban da malaman makarantar sun yi nasarar tsere wa ne daga hannun maharan bayan da hayaniyar ta basu alamar cewa wani abu na faruwa.

Exit mobile version