Kaka-ni-ka-yin Da Yajin Aikin Likitoci Ya Jefa Majinyata

Likitoci

Daga Khalid Idris Doya,

A ranar Litinin din da ta gabata ce, kungiyar Likitoci ta kasa ta shiga wani yajin aikin sai abin da hali ya yi na gama gari wanda kusan kowace jiha sai da wannan lamarin ya shafa. Wannan matakin ya jefe majinyata da suke faman jinya a manya da kananan asibitoci a fadin kasar nan cikin halin ni-‘yasu.

 

Ita dai kungiyar ‘National Association of Resident Doctors’ (NARD) ta shiga yajin aikin ne bisa bukatun da suke kukan gwamnatin tarayya ta ki cika musu da suka hada da na albashi, alawus-alawus, inganta walwala da kyautata yanayin aiki ga mambobinsu da sauran batutuwan da ya shafesu kai tsaye.

 

Wannan yajin aikin dai shi ne kusan karo na hudu da likitocin ke tsunduma a shekara guda, ba wani sabon labari ba ne tafiyar Likitoci yajin aiki a wannan kasar duk kuwa da gayar alfanunsu wajen kula da kiwon lafiyan ‘yan kasa.

 

A bisa haka ne muka shirya rahoton musamman domin jin irin halin da majinyatan suka samu kansu a ciki. Koda yake, a wani binciken da LEADERSHIP A YAU ta gudanar ta iya gano cewa, ma’aikatan wucin gadi da sauran rassan jami’an lafiya, suna iya bakin kokarinsu wajen kula da majinyata, amma muhimman abubuwan da suka shafi likita ne zai yi su kai tsaye sun tsaya cak.

 

Wasu asibitocin da muka ziyararta a jihohin kasar nan, mun iya gano cewa wasu majinyatan suna fuskantar ganin likita kan halin da suke ciki na jinya, ammma sai wannan yajin aikin ya shigo, a bisa hakan matakin kula da lafiyarsu ya zame musu da wuya matuka.

 

Wani binciken da muka yi, mun iya gano cewa a irin wadannan asibitocin da yajin aikin ya shafa a fadin kasar nan, akwai wasu manyan likitoci da su kuma yajin aikin bai shafa ba, amma ba su da yawan da za su iya kula da adadin majinyatan da suke kwance a asibitocinsu, kai tsaye yajin aikin likitocin ya yi tasiri wajen galabaitar da manjinayata a kusan dukkanin asibitocin da suke fadin kasar nan.

 

Wasu wadanda a halin yanzu suke kwance a asibitoci daban-daban a Bauchi, Ondo, Umuahia, Legas, Ibadan, Akure, Illorin, Ado-Ekiti da Jihar Sakkwato da wasu da dama domin jinyan cututan da ke damunsu dukka labarin iri daya ne, sun nuna damuwarsu bisa yajin aikin tare da bukatar bangarori biyu na gwamnati da kungiyar likitocin da su samu fahimtar juna domin ganin an janye wannan yaji aikin saboda bunkasa kiwon lafiyar al’umma.

 

Wasu majinyata da ke kwance a wani asibitin gwamnati da ke babban birnin Abuja, sun ce sun shiga damuwa saboda kauracewar likitocin da ya kamata su ci gaba da duba lafiyarsu.

Wani magidanci da ke kwance a babban asibitin Gwarimpa ya ce, babu likita ko daya da ya je babban dakin maza da suke kwance tun kashegarin ranar da suka tafi yajin aikin, alhali kuma sun saba zuwa don ganin halin da suke ciki.

 

“Sai magungunan da ke nan kawai aka ba ni. Jikina akwai dai dan sauki amma tun da babu likitoci, muna cikin damuwa,” in ji majinyacin da ba a ambaci sunansa ba.

 

Shi ma wani da ke jinyar kafarsa da ta karye a asibitin na Gwarimpa da ke Abuja ya ce yana fargabar lafiyar kafarsa wanda ya kamata ta samu kulawar likita duk bayan kwana biyu zuwa uku.

 

Ya ce masifar yajin aikin likitoci ba abu ne mai kyau ba a gare su. Don haka ya yi kira ga bangarorin biyu su daure su sasanta.

 

Wasu majinyatar da aka sallamesu bisa dole duba da tsananin jinyar da suke fama da su walau don su sauya asibitoci zuwa na masu zaman kansu ko wasu ‘yan dabaru na daban ko kuma komawa gida domin neman lafiya. Haka kuma, hukumomin asibitocin da dama sun nuna damuwarsu bisa irin tasirin da wannan yajin aikin ya yi da suka nemi a shawo bakin zare, inda su kuma kungiyar NARD suka ce atafau ba za su janye ba har sai gwamnati ta yi abun da ya dace.

 

A babban asibitin koyarwa ta jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da kuma asibitin gwamnatin tarayya da ke Azare (FMC), harkokin kula da lafiya duk sun gamu da tsaiko a bisa wannan yajin aikin kamar yadda wakilinmu ya binciko.

 

Sashin kula da majinyata da dama kama daga irin dakunan kula da maza, manya, yara, dakin tiyata, dakin haihuwa da sauran sassa majinyata suna zaman neman dauki da agajin likitoci a hali da ake ciki.

 

A ziyarar gani da ido zuwa asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Owo a jihar Ondo, mambobin kungiyar likitoci sun kaurace wa wuraren aikinsu dukka a cikin wannan yajin aikin nasu.

 

Wasu daga cikin likitocin da suka gana da ‘yan jarida sun nuna damuwarsu bisa rashin cika alkawuran da gwamnatin tarayya ta musu, suna masu misalta hakan da sanyaya musu guiwa a kokarinsu na sadaukar da kai wajen hidimta wa kasa da ‘yan kasa.

 

A asibitin Usmanu Danfodio ta (UDUTH) kuwa, manyan likitoci da ba su da yawa da nas-nas ne suka dukufa wajen taimaka wa majinyata, inda kuwa wasu majinyatan iyalansu suka ba su shawara su nemi mafita walau na zuwa asibiti mai zaman kansa don neman jinya ko wata hanyar ta daban.

 

Wani majinyaci a asibitin mai suna Aminu Abdullahi, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, halin da majinyata suka samu kansu a halin yanzu ya tsananta domin tsananin jinya da kuma rashin likitocin da ke duba su.

 

Ya roki gwamnatin tarayya da likitocin da su sasanta tsakaninsu domin majinyaci ya samu saukin jinyar da ke fama da shi a halin yanzu.

 

Wasu majinyata da dama, sun ce muddin ana son rayuwarsu ta ci gaba, to fa kungiyar da hukumomi sai sun fahimci juna domin yanayin jinyar da suke fama da su a halin yanzu, inda suka ce, komai na kula da lafiyarsu na neman tsayawa domin sai likita ya dubasu kafin ya bayyana meye nas-nas za su musu ko kuma wani irin magani ya dace a sayo musu don neman lafiya da sauki.

 

Shugaban kungiyar NARD na kasa, Dakta Okhuaihesuyi Uyilawa, ya ce ba za su janye wannan yajin aikin ba har sai hakarsu ta cimma ruwa, yana mai cewa ba su da wani zabin da ya wuce hakan.

 

Uyilawa, ya kuma ce wasu likitoci a halin yanzu suna fuskantar rashin albashi kama daga masu bin na wata biyu wasu ma har zuwa watanni 18 ba tare da an biya su ba. Yana mai cewa, “ku yi tunanin halin da iyalan likitan da ya rasa albashin wata 18 za su shiga.”

 

Ya dai zargi gwamnati da nuna rashin gaskiya da kuma gaza cika alkawari daga bangarenta, lamarin da a cewarsa ya tilasta musu daukar wannan mataki ba wai tare da suna son hakan ba.

 

Dakta Uyilawa, ya ce, “tun kwanaki 115, yarjejeniyar da muka cimma da gwamnati har yanzu ba a aiwatar da su ba. Mun rasa likitoci 19 sakamakon annobar Korona, amma iyalansu suna nan suna fama da rayuwa, inda a halin yanzu suke neman agaji da tallafi kan yunwa da ke kokari cin karfinsu.”

 

Ya ce, sun sadaukar da rayukansu wajen yaki da cutuka ciki har da Korona, ammma alawus din shiga hatsari bai taka-kara ya karya ba da ake ba su.

 

Ya nemi ‘yan kasa da cewa su matsa wa gwamnatin tarayya don ta cika musu alkawuran da suka yi domin ganin sun dawo bakunan aikinsu.

 

A gefe guda kuma, gwamnatin tarayya ta roki likitocin da su dawo teburin sulhu domin tattaunawa kan batutuwan da suke akwai.

 

Ministan lafiya, Dakta Olurunnimbe Mamora, shi ne ya yi rokon a madadin gwamnatin tarayya, inda ya nemi kungiyar ta NARD da ta amince da tayin da suka yi mata domin dawowa teburin tattaunawa wajen ci gaba da baje batutuwan da suke jibge don yi wa tufkan hanci da warwarewa cikin laluma da salama.

 

Ministan wanda ke rokon yayin bude wani taron ganawa na shekara-shekara ta 2021 na Scientific Conference of the Nigeria Medical Association (NMA), reshen babban birnin tarayya (FCT) da ya gudana a Abuja.

NARD dai ta shiga yajin aikin gama-gari ne a ranar 2 ga watan Agustan 2021 domin matsa kaimi ga gwamnatin tarayya don cimma yarjejeniyar da suka sanya hannu a kai tun a watan Maris din 2021 da suka shafi walwala da jin dadin mambobinta.

Mamora ya kara da cewa, ta hanyar tattaunawar, za a samu yanayin da za a fahimci juna tare da shawo kan matsalolin don ganain kiwon lafiyan jama’a bai samu nakasu ba, yana mai rokon kungiyar da ta amince da hakan domin alfanunsa ga sashin kiwon lafiya.

Ya ce, “ina karfafanku da ku amince da wannan tayin domin ganin kiwon lafiyan jama’a ya samu habakuwa a maimakon barinsa ya fada cikin garari.

“Akwai muhimmanci a dawo teburin tattaunawa domin yayyafa wa batutuwan nan ruwan sanyi, ina rokon abokan aikinmu da su rungumi tayin nan namu. Sulhu din nan za ta taimaka sosai musamman a irin wannan lokacin da kasar nan take gayar bukatar azamar likitoci.”

Ministan ya kuma nanata cewa, gwamnatin tarayya a shirye take wajen bada gudunmawa domin dakile cutukan da suke yaduwa da wadanda suke addabar jama’an kasa.

Kawo zuwa yanzu dai marasa lafiya da dama a fadin kasar na cikin zullumi da neman mafita, inda masu yawansu suka yi ta rokon gwamnati da kungiyar likitoci da su sasanta tsakaninsu.

Exit mobile version