Khalid Idris Doya" />

Kakakin Gwamnan Bauchi Ya Tsallake Rijiya Da Baya

A daren ranar Litinin din nan da ta gabata ne Malam Ali M. Ali ya tsallake Rijiya da baya a sakamakon wani mummunar hatsarin mota da ta rutsa da shi a hanyarsa ta dawowa cikin Bauchi daga karamar hukumar Jama’are.
Ali M. Ali wanda shi ne babban mai magana da yawun gwamnan jihar Bauchi kuma mai taimaka masa wajen tsare-tsare da hulda da ‘yan jarida, ya gamu da hatsarin motar ne da shi da direbansa Manu Direba.
Wakilinmu ya shaida mana cewar Ali M. Ali ya bugu sosai a kirjinsa, inda shi kuma Direban nasa ya karye har wuri biyu, daya a hanu daya kuma a kafa.
Rahotonni sun zo kan cewar hatsarin ta rutsa da kakakin gwamnan ne a daren ranar Litinin din a lokacin da ke kan hanyarsa ta dawowa cikin Bauchi daga karamar hukumar Jama’a, bayan wani aikin musamman da ya je yi.
Rahoton ya shaida cewar an garzaya da marasa lafiyan zuwa babban asibitin koyarwa ta Abubabakar Tafawa Balewa Teaching Hospital, da ke Bauchi, domin samar musu da kulawar likitoci na gaggawa.
Kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Bauchi, Alhaji Umar Ibrahim Sade ya tabbatar wa ‘yan jarida aukuwar lamarin, inda yake mai shaida cewar, “Lallai abokin aiki Ali M Ali ya gamu da hatsarin mota, amma kawo yanzu da shi da direbansa suna kan amsar kulawar likitoci.
Ya kara da cewa, “Direban nasa ya karye a kafa da hanu, shi kuma Ali (Kakakin gwamnan) ya bugu sosai ne a karjinsa,” Inji shi, sai dai ya yi musu fatan samun sauki daga wajen Allah madaukakin Sarki.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci Malam Ali Muhammad Ali a gadon jinya ya tarar da shi na faman jinyar buguwar da ya yi, duk da wakilinmu ya tabbatar mana Malam Ali na iya tantance komai amma yana jin zafin bugun kirjinsa sosai, domin kuwa buguwar ta shige sa sosai.

Exit mobile version