Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Yi Jawabi Game Da Zubar Da Gurbataccen Ruwan Tashar Nukiliyar Fukushima A Teku

Daga CRI Hausa

A yau ne, gwamnatin kasar Japan ta tsai da kudirin zubar da gurbataccen ruwan tashar makamashin nukiliya ta Fukushima a cikin teku. A wannan rana, kakakin maaikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi jawabi game da wannan batu, inda ya yi nuni da cewa, a matsayinta na kasa mai makwabtaka da kasar Japan da kuma kasar da moriyarta take da nasaba da kasar Japan, Sin ta sa lura sosai game da wannan batu.
Kakakin ya bayyana cewa, hadarin dake tattare da tashar samar da wuta ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta Fukushima daya ne daga cikin manyan hadarori mafi tsananni a duniya, wanda ya haddasa zubar abubuwan nukiliya da dama, wadanda suka kawo illa ga yanayin teku, da ingancin abinci, da kuma lafiyar jikin dan Adam. Kakakin ya yi nuni da cewa, kasar Japan ta ki daukar matakan daidaita ruwan, da kuma yin biris da raayoyin nuna kin amincewa daga al’ummu cikin gidan kasarta da kuma kasashen waje, da gaza yin shawarwari tare da kasashe masu makwabtaka da ita da sauran kasashen duniya, da kuma zubar da gurbataccen ruwan a cikin teku, ta dauki wannan mataki ne ba tare da yin laakari da nauyinta da ta dauka bisa wuyenta ba, wanda zai kawo babbar illa ga lafiyar dan Adam da kuma moriyar jamaa da kasashen dake makwabtaka da ita. (Zainab)

Exit mobile version