Kakakin Majalisar Bauchi Ya Bukaci ATAP Ta Janye Yajin Aikin Da Take Kai

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Yakubu Sulaiman, ya kirayi kungiyar malaman kwalejin kimiyya reshen kwalejin kimiyya mallakin gwamnatin Jihar Bauchi (ATAP) da su dakatar da yajin aikin da suke kan yi domin dalibai su samu zarafin cigaba da harkokin karatunsu.

Sulaiman ya yi wannan bukatar ne a lokacin da ya kira taron ganawa da hukumar gudanarwa na kwalejin a karkashin Rector Dakta Alhaji Adamu Sa’idu, da jagororin kungiyar ASUP reshen ATAP bisa jagorancin shugabanta Malam Dahiru Musa a gidansa da ke Bauchi.

A sanarwar manema labarai da Abdul Ahmad Burra, mai magana yawun Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi, ya fitar tare da rabar wa ‘yan jarida a Bauchi jiya, ya bayyana cewar, zaman dalibai a gida da kuma yajin aikin da suke kan yi ka iya gurgunta musu iliminsu da kawo nakasu ga cigaban ilimi, yana mai cewa akwai bukatar komawa aji domin cigaba da basu darussa.

Abubakar Sulaiman ya nuna matukar damuwarsa da cewa dalibai sun shafe tsawon lokaci suna hutun dole na kariya daga cutar Korona don haka bai kamatu kuma bayan hakan ba wani yajin aiki ya cigaba da faruwa, yana mai nuna damuwa kan halin ilimin daliban.

Abubakar ya ce shi da mambobin majalisar dokokin jihar sun damuwa sosai da halin ilimi a jihar kuma a shirye suke su cigaba da bada gudunmawa domin ganin ilimi ya inganta.

Kakakin ya lura akwai bukatar kai maganar zuwa gaban gwamnan Jihar Bala Muhammad domin ganin an biya bukatun da malaman ke nema don shawo kan wannan yajin aikin da suke kai din, kan hakan ne ma da kansa ya yi maganar da gwamnan.

“Na kai batun zuwa gaban gwamna wanda na ke da yakinin zai dauki matakan da suka dace a kai, don haka ina rokonku da ku gaggauta janye yajin aikin nan domin ‘ya’yanmu su samu koma bakin aikin daukan darasi na neman ilimi.

“Gwamna ya yi muhimman ayyuka ga sashin ilimi kuma na tabbata na aiki tukuru wajen shawo kan matsalar albashi a jihar. Kwamitin mataimakin gwamna na aiki sosai wajen ganin ya shawo kan dukkanin matsalolin da suke akwai a sashin albashi kuma nan kusa za su kammala aikin nasu,” Kakakin ya bada tabbaci.

Da yake maida jawabi, Shugaban kwalejin, Dakta Adamu Saidu, ya gode wa Kakakin majalisar bisa shiga cikin lamarin wanda ya misalta shi a matsayin mai kishin jiha da cigabanta.

A cewarsa, hukumar gudanar ta yi duk iya kokarinta wajen ganin an kauce wa shiga yajin aikin domin tabbatar da an daidaita harkokin karatun da hutun korona ya jawo amma ASUP ta nace sai fa ta tsunduma.

Ya roki kungiyar malaman kwalejin da ta duba kirayen-kiranyen masu ruwa da tsaki ta janye wannan yajin aikin yayin da kuma za a ci gaba da kokarin cike musu bukatunsu da suke nema.

Da yake maida jawabinsa, shugaban ASUP reshen ATAP, Malam Dahiru Musa, ya jinjina wa namijin kokarin Kakakin Majalisar bisa damuwa da yayi kan lamarin dalibai da na kungiyar.

A daidai lokacin da yake yaba wa Kakakin da shugaban ma’aikatan jihar bisa shiga cikin lamarin, ya hore su da su dauki bukatun nasu a rubuce domin kaiwa gwamna domin ganin an aiwatar da su.

Dangane da bukatar da Kakakin majalisar ya musu na batun janye yajin aiki, ya bayyana cewar za su dauki batun kana su kai ga mambobin kungiyar nasu domin ganin an dauki matakan da suka dace na shawo kan lamarin.

Exit mobile version