Kakakin Majalisar Wakilai Zai Koyar A Sakandaren Katsina

Femi Gbajabiamila, Shugaban Majalisar Wakilai, zai koyar da dalibai a wata makarantar sakandiren gwamnati da ke jihar Katsina – Gbajabiamila ya fara aikin koyar wa na ‘sa kai’ a mazabarsa, Surelere 1, a Jihar Legas a cikin shekarar 2017 – A cewar mai taimaka a bangaren yada labarai, shugaban majalisar zai koyar makarantun sakandire a dukkan sassan Najeriya Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, zai koyar a babbar makarantar sakandiren ‘Pilot’ da ke kofar Sauri a jihar Katsina.

Gbajabiamila ya fara aikin koyar wa na ‘sa kai’ a mazabarsa, Surelere 1, a jihar Legas a cikin shekarar 2017, lokacin yana rike da mukamin Shugaban masu rinjaye a zauren majalisa. A cewar Lanre Lasisi, mai taimaka wa Gbajabiamila a bangaren yada labarai, Shugaban majalisar zai koyar makarantun sakandire a dukkan sassan Najeriya.

Lasisi ya ce Gbajabiala zai koyar da daliban makarantar sakandiren unguwar Kofar Sauri ‘illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi, wanda dama darasi ne a cikin manhajar daliban ta wannan sheakarar. Bayan koyar wa a makarantar sakandiren, Gbajabiamila zai ziyarci wasu mazauna sansanin gudun hijira a sansaninsu da ke jihar Katsina.

Kazalika, Shugaban majalisar zai gana da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, da wasu shugabannin jama’ da kuma kungiyoyin matasa dabadaban a jihar. Gbajabiamila ya isa jihar Katsina domin koyar da daliban da kuma ganawa da gwamna Masari da sauran harkokin da zai gudanar a jihar, kamar yadda ya ke a cikin sanarwar da mai taimaka masa a bangaren yada labarai ya fitar.

Exit mobile version