Game da yadda wasu mutane ke ci gaba da yada jita-jita cewa, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” (BRI) ta kasar Sin na sanya wasu kasashe fada cikin “tarko na bashi”, mista Wang Wenbin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Litinin cewa, har zuwa yanzu, babu wata kasar da ta sa hannu kan yarjejeniyar BRI da ta yarda da maganar “tarko na bashi”.
A cewar Wang, an gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” don karfafa hadin gwiwar kasashe daban daban a fannin tattalin arziki, tare da zummar samun ci gabansu tare. Cikin wadannan shekaru 7 tun bayan da aka gabatar da shawarar, tana samun karbuwa sosai a duniyarmu.
Jami’in ya kara da cewa, sakamakon yaduwar cutar COVID-19, da karayar tattalin arzikin duniya, wasu kasashe masu tasowa suna fuskantar matsala wajen samun bashi da yawa. Ganin haka ya sa kasar Sin ta soke wasu basukan da take bin wasu kasashen dake nahiyar Afirka, har ma ta zama kasar da ta samar da mafi yawan gudunmawa a fannin aiwatar da shawarar rage bashi da kungiyar G20 ta gabatar. Sai dai wadanda suka fi samar da basuka wasu hukumomin hada-hadar kudi ne, gami da wasu kasasashe masu sukuni. Ya kamata su ma su shiga shirin rage bashin da ake bin irin wadannan kasashe, in ji kakakin kasar Sin.
Ban da wannan kuma, Wang Wenbin ya ce, batun da wasu ke yayatawa wai, kasar Sin tana leken asiri a hedkwatar kungiyar Tarayyar Afirka (AU), labari ne na bogi, kuma tuni kawayen kasar Sin da suka hada da hukumar gudanarwar AU da galibin shugabannin kasashen na Afirka, suka yi fatali da shi.
Da yake karin haske kan wannan batu, yayin tambayar da aka yi masa, Wang Wenbin ya jaddada cewa, wasu masu surutu a gyefe, ba za su taba lalata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ba, kuma labaran karya ba za su lalata abokantakar dake tsakanin sassan biyu ba. A shekarar 2020, hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskanci sarkakiya. Bayan da annobar Covid-19 ta barke ba zato ba tsammani, sassan biyu sun taimakawa juna don shawo kan matsalolin da suka kunno kai. (Bello / Ibrahim)