Abubakar Abba" />

Kakar Noman Bana: Yadda Manoma Za Su Iya Samun Taki

Daga Abubakar Abba

Ganin cewar damunar bana sai kara kunno kai take a wasu yankunan kasar nan, an yi dubi akan shirye-shiryen da masu ruwa da tsaki suke kan yi wajen samar da kayan aikin noma, musamman ingantaccen takin zamani da iri ga manoma.

Shugaban kungiyar dilolin samar da kayan aikin noma na kasa wadanda suka fi samar da kayan na noma Alhaji Kabiru Fara, ya bayyana cewar, suna da isasashen takin zamani a kasa, da zai wadatar da manoma miliyan goma don kakar noman na bana.

A hirar da aka yi dashi Fara a ranar Litinin data gabata ya jadda da cewar, suna gudanar da ayyukan su a mataki biyu, wanda ya hada da, budaddiyar kasauwa, inda suka saba gudanar da kasuwancin su da kasuwar ta bayar da tallafi da gwamnati ta kayyade yawan kayan aikin da manoma za su samu.

Ya ci gaba da cewa, a mataki na farko, suna da isasshen takin zamani a karkashin shirin fafar gwamnatin tarayya na manoma (PFI) wanda manoman wakilai suka riga suka yi rijista don saye da kuma sayarwa.

Shugaban ya kara da cewar, matakin na biyu kuma shine akwai shiri na gwamnati da ake kira(GES), inda gwamnatin ta lissafa manoma a daukacin fadin kasar nan don su biya kashi 50 bisa dari na tsada gwamnati za ta biya  mu biya kashi 50 bisa dari.

Ya bayyana cewar, “ don har yanzu ana kan gudanar da shirye-shirye kuma muna jiran umarni na karshe daga gwamnati tarayya don mu karba don ya hada da rabar da kayan aikin noman ga daukacin kananan hukumomi guda 774 da ake dasu a kasar nan.

Ya bayyana cewar, amma a yanzu muna gudanar da namu kasauwancin ne a budaddiyar kasuwa.

Da yake tsokacin akan adadin manoman da za su amfana a wanan shekarar a karkashin shirin na (GES) na bayar da tallafi, Shugaban yace, gwamnati ce za ta yanke shawara akan ko manoma nawa ne take so.

Shugaban ya kara da cewar, a kakar noman bara, manoma 500,000 aka sanya a noman rani, mai makon manoma miliyan 2.5.

Ya bayyana cewar, mai yi wa gwamnati ta sanya manoma miliyan goma.

Akan iri kuwa, Shugaban ya bayar da dalilin da yasa ingantaccen iri zai yi karanci, ya kara da cewar, har yanzu gwamnati ce ke da kamfanonin irin wato ma’ana da yawansu baza su iya samar da ingantaccen irin da ake bukata ga mamoman a bisa rangwame ba.

Ya yi nuni da cewar, akwai bukatar a baiwa masu samar da kwarin gwiwa.

Shi kuwa Shugaban shirin samar da taki na fadar Shugaban kasa Mista Thomas Etuh, a satin da ya gabata ya bayyana cewar, shirin na (PFI) zai samar da tan miliyan daya na taki sunfirin NPK a kakar noman shekarar 2018.

Kamfanin sarrafa takin zamani na Indorama Eleme Fertilizers da kuma kamfanin samar da magungunan noma wadanda sune ke akan gaba wajen  a samar da takin zamani sunfurin Urea a kasar nan, ya tabbatar tsarin da yake dashi na kara yawan taki sunfurin Urea ga manoman kasar nan da zai kai yawan 750,000 a kakar noman na bana.

Wannan wani kari ne da zai kara yawan takin sunfurin da kamfanin ya yi niyyar samarwa da gwamnatin tarayya daga yawan 180,000 da aka samar a shekarar data gabata zuwa 360,000 a cikin wannan shekarar don sarrafa takin sunfurin NPK.

Exit mobile version