Kungiyar kwallon kafa ta jihar Filato, wacce aka fi sani da Plateau United ta lashe kofin kakar wasan Nijeriya na bana, a karon farko kungiyar ta samu nasarar ne a yau Asabar bayan ta doke kungiyar Enugu rangers da ci biyu da nema wanda shi ya kawo karshe wasanni 38 da aka buga a kakar wasan.
Wannan nasarar da kungiyar ta yi ya zama tarihi gare ta, domin kafin yanzu bata taba lashe gasar wasan ba shekaru da dama bayan kafa kungiyar, ita dai kakar wasan kungiyoyi 20 ne suka shiga gasar.
Plateau United ta samu nasara ne da maki 66 a wasanni 38 da ta buga.