Connect with us

LABARAI

Kakkarfar Iska Ya Haifar Da Mutuwar Mutum Bakwai A Yobe

Published

on

Sakamakon wani kakkarfan iska a jihar Yobe, ya jawo mutuwar kimanin mutum bakwai (7), wasu karin mutane 45 sun samu raunuka tare da hankade gidaje, akalla 100, a sassan jihar, wayewar garin ranar Larabar da ta gabata.

Da yake tabbatar da al’amarin, shugaban hukumar bayar agajin gaggawa a jihar Yobe (SEMA), Dr Muhammed Goje ya bayyana cewa, hukumar su ta dauki matakin da ya dace a lokacin da abin ya faru, tare da shaidar da cewa kimanin mutum 45 su ka kai asibiti don samun kular likita.

“Sannan kuma, daga cikin wannan adadin mutum bakwai (7) da su ka mutun, shida (6) daga cikin su sun fito ne daga karamar hukumar Fune, yayin da dayan ya rasa ransa ne a birnin Damaturu.” In ji Dr Goje.

Haka kuma, Dr. Goje ya kara da cewa, SEMA ta na aiki tukuru wajen gano kamar barnar da kakkarfan iskan ya jawo, kana ya ce za su dauki matakin bai wa jama’ar da lamarin ya shafa da kayan tallafin gaggawa- abinci, magunguna, da kayan gini.

Bayanan da Leadership A Yau Jumu’a ta tattara a jihar, kakkarfan iskan tare da ruwan sama, ya fara ne da kimanin karfe 7:00 na dare, wanda kuma ya dauki awanni ya na gudana tare da jawo asarar miliyoyin Naira.

Bugu da kari kuma, kakkarfan iskan ya shafa sun hada da kananan hukumomin, Damaturu babban birnin jihar, Tarmuwa, Potiskum, Fune, Bursari da Nguru.o

Bisa ga hakan ya jawo jama’a da dama sun bayyana alhinin su dangane da wannan ja’ifar. Daga cikin akwai Baba Modu Mellah, magidanci ne ya bayyana cewa, kakkarfan iskan ya tunbuke baki dayan rufin kwanon gidan su, wanda yanzu haka a wayam su ke.

A hannu guda kuma, shima Malam Bulama Isa, mai unguwar Sabon Kwalta Plmpamari a Damaturu, ya shaida wa wakilin mu cewa, kimanin sama da magidanta 20 ne su ka rasa gidajen su, ta dalilin wannan kakkarfan iskan.

Malam Isa ya kara da cewa, sannan wadanda wannan ja’ifar ta shafan ya kasance ba su da wani zabi face dole sun koma da zama rakabewa a gidajen makobta.

Da ya ke bayyana alhinin shi dangane da ta’adin da kakkarfan iskan ya yi, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya mika jajen shi bisa ga faruwar ja’ifar da ta yi sanadiyar rasa rayukan jama’a, wasu da dama sun samu raunuka tare da barnata gidajen jama’a da asarar miliyoyin naira a jihar.

Sanarwar, mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai, Mamman Mohammed, Gwamna Buni ya bai wa hukumar ayyukan gaggawa a jihar (SEMA) umurnin kula da wadanda su ka samu raunukan, da binciko kimar asarar da kakkarfan iskan ya jawo.
Advertisement

labarai