Kalamai Marasa Kyau A MDD Ba Za Su Hana Mutane Su Fahimci Ainihin Xinjiang Ba
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kalamai Marasa Kyau A MDD Ba Za Su Hana Mutane Su Fahimci Ainihin Xinjiang Ba

byCGTN Hausa
2 years ago
MDD

Jiya Talata ne a birnin Geneva na kasar Switzerland, yayin da take halartar taron bita na hudu na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, kasar Sin ta gabatar da tsarin raya hakkin dan Adam da kuma nasarorin da ta cimma. Fiye da kasashe 120 sun furta kalamai masu kyau. Wannan ya kawo cikas ga wasu tsirarrun kasashen yammacin duniya wadanda suka yi kokarin siyasantar da batun nazarin kare hakkin dan adam ta hanyar wasu batutuwa irin su jihar Xinjiang ta kasar Sin. Har ila yau, a jiyan kasar Sin ta fitar da wata farar bayani mai taken “Tsarin shari’a da kuma ayyukan yaki da ta’addanci na kasar Sin”, wanda ya yi cikakken bayani kan ayyukan yaki da ta’addanci da kasar Sin ta samu.

Masanan da abin ya shafa sun ce, idan aka yi la’akari da abin da wannan takarda ta kunsa, za a fahimci cewa, yaki da ta’addanci kamar yadda doka ta tanada a ko’ina, ba wai kawai yakar ta’addancin da ke jefa rayuka da dukiyoyin jama’a cikin hadari ba ne, har ma yana kare hakkin jama’a na rayuwa, samun ci gaba da sauran hakkokin da suka shafi bil-Adama.

Ta’addanci abokin gaba ne na bil-Adama, kuma kasar Sin ta yi fama da wannan matsala. Tsoro, hasarar rayuka, ci gaba, wadannan sakamakon sun bayyana a fili cewa, yaki da ta’addanci bisa doka ne kawai zai iya kare hakkin bil-Adama. Ruhin bin doka da oda a yaki da ta’addanci na kasar Sin, ya yi daidai da ka’idoji da ra’ayoyin yaki da ta’addanci na kasa da kasa. Ba wai kawai ya hana da hukunta ayyukan ta’addanci yadda ya kamata ba, har ma da mutuntawa da kare hakkin dan Adam yadda ya kamata. Wasu kasashen yammacin duniya, suna amfani da “ma’auni biyu” wajen yaki da ta’addanci da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, ta hanyar fakewa da batun “doka” da “yancin dan Adam”, wanda ba wai kawai yana kawo cikas ga hadin gwiwar yaki da ta’addanci na kasa da kasa ba, har ma da gurgunta hadin gwiwar kare hakkin dan Adam na duniya. (Mai fassara: Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Ana Tuhumar Sojoji 30 Kan Yunkurin Juyin Mulki A Saliyo

Ana Tuhumar Sojoji 30 Kan Yunkurin Juyin Mulki A Saliyo

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version