Al’ummar Musulmi a fadin duniya suna ta kaurace wa kayayyakin da suka fito daga kasar Faransa, sakamakon kalaman batanci da Shugaban Kasar, Emmanuel Macron ya yi, a yayin da Macron din yake kare zane-zanen batanci da akayi don cin mutumcin Annabi (S).
Macron din ya alakanta addinin Musulunci da ta’addanci, sannan ya sha alwashin dakile abinda ya kira da tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci a kasar ta Faransa, wanda ya jawo zanga-zanga a kasashen duniya da dama, har ta kai ga Musulmi a fadin duniya suna kira da a kaurace wa duk kayan da suka fito daga kasar ta Faransa.
Shugaban kasar Turkiyya, Erdogan ya bukaci Musulmi da su kaurace wa duk kayan kasar ta Faransa, inda yake cewa; Ina kira ga dukkan al’umma su kaurace wa kayan kasar Faransa, sannan ya wajaba shugabannin kasashen Turai su taka wa Macron birki ya daina kalaman batanci ga Musulunci.
Tuni har al’ummomi a kasar Kuwait sun fara kaurace wa kayan kasar ta Faransa, inda fiye da manyan kantina suka kafe allon shaida da ke nuna sun daina siyar da kayan kasar Faransa, haka ma abin yake a kasar Jordan, a Kasar Qatar ma dai haka abin yake, babbar jami’ar kasar Qatar ta soke wani taro da za ta yi da hadin gwiwa da kasar ta Faransa.
Ma’aikatar waje ta kasar Faransa, ta bayyana kauracewar a matsayin rashin kyautawa, inda ta bukaci a gaggauta janye wannan kauracewar. A cewar ma’aikatar kalaman Macron sun dace da ‘yancin ra’ayi, ‘yancin fadin albarkacin baki, ‘yancin addini da kuma dakile kiyayya. A ra’ayin ma’aikatar wannan matakin da Macron din ya dauka, mataki ne na yaki da tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci.
Kasashen Jordan, Iran, Pakistan, da Masar sun yi Allah-wadai da kalaman da Macron, “Mun yi tir da zane-zanen jaridar kasar Faransa, da kalaman Macron, inji Ministan Harkokin Wajen Kasar Jordan.