Connect with us

LABARAI

Kalaman Batanci: Yari Zai Maka Fani Kayode A Kotu

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana cewa zai dau matakin Shari’a kan tsohon ministan sufurin sama, Mista Fani Kayode, sakamakon wata kasassaba da Fani din ya yi kan Yari. Fani-Kayode ya caccaki Yari ne a shafin sada zumuntar shi na Twitter mai suna @realffk.

Hadimin Yari na musamman, Moyuwa Oluwabiyi ne ya saki wannan sanarwar a yau Alhamis, inda ya ke cewa; kowa ya san tsohon Gwamna Yari dan kasa ne mai kiyaye doka, wanda baya wani aiki na saba dokokin kasa.

Kalaman na Fani-Kayode sun biyo bayan zargin da aka yi wa Yari na taka dokokin kiyaye yaduwar cutar Korona a filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Kano, inda hadimin gwamnan ya ce; wannan lamarin bai faru ba, don haka Fani-Kayode ya kwana da shirin ji daga kotu kan caccakar Yari da ya yi ba gaira babu dalili.
Advertisement

labarai