CRI Hausa" />

Kalaman Kwararrun WHO Game Da Dakin Gwajin Kwayoyin Cuta Na Wuhan Sun Bata Ran Yammacin Duniya

A ranar 3 ga wata, tawagar kwararrun hukumar kiwon lafiyar duniya WHO ta shafe kusan sa’o’i hudu a cibiyar nazarin kwayoyin cuta dake birnin Wuhan na kasar Sin, baya ga ziyartar dakin gwajin kwayoyin cuta. Kamfanin dillancin labarai na Sputnik na kasar Rasha ya bayyana a jiya cewa, Dakta Vladimir Dedkov, kwararre a fannin ilmin cututtuka masu yaduwa, kana mambar tawagar kwararrun WHO, kuma mataimakin shugaban cibiyar nazari na Pasteur da ke Saint Petersburg a kasar Rasha, ya nuna shakku kan kalaman da aka yi a baya cewa, wai kwayoyin cutar COVID-19 sun fito ne daga dakin gwajin.
A cewarsa, kayayyakin dake dakin gwajin kwayoyin cuta na Wuhan su na da matukar inganci, kuma babu wanda zai iya fitar da wani abu daga cikinsa.
Game da kasuwanni da ke birnin Wuhan, Dakta Dedkov ya bayyana cewa, ko da ana zaton kwayoyin cutar COVID-19 sun samo asali ne daga wasu wurare, amma yanayin kasuwar sayar da amfanin teku na Hua’nan da ke birnin na iya taimakawa yaduwar cutar.
A ranar 3 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya furta cewa, tawagar kwararrun WHO da bangaren kasar Sin sun tattauna sosai, har ma tawagar ta ziyarci cibiyar nazarin kwayoyin cuta dake Wuhan, a kokarin gano asalin kwayoyin cutar. Ko da yaushe Sin na hada kai tare da WHO bisa ka’idojin gudanar da komai ba tare da rufa-rufa ba, da sauke nauyin da ke wuyanta.(Kande Gao daga sashen Hausa na CRI)

Exit mobile version